✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isa sansanin gyaran hali na Gombe

  Gwamnatin Tarayya ta fara karbar mayakan kungiyar Boko Haram da suka mika wuya bayan yi musu tayin afuwa inda take shirin ba su horo…

 

Gwamnatin Tarayya ta fara karbar mayakan kungiyar Boko Haram da suka mika wuya bayan yi musu tayin afuwa inda take shirin ba su horo su zamo ’yan kasa nagari ta hanyar koya musu sana’o’i da sauya musu tunani.

Gwamnatin wadda ta aike da kashi na farko na tubabbun ’yan Boko Haram din shida zuwa wani sansani a Jihar Gombe inda aka horar da su na wata hudu ta sake turo maza 52 da mace daya zuwa sansanin a ranar Asabar da ta gabata a cikin jirgin saman yaki na soja mai lamba NAF 913 sai matar wadda ba a ciki jirgin aka kai ta ba inda suka wuce sansanin don ba su kulawar da ta dace.

Tubabun ’yan Boko Haram din na isa sansani aka fara tantance su inda aka shiga da su wajen daukar bayanai da duba lafiyarsu kafin a wuce da su wani daki inda aka yi musu katin zama dan kasa domin fara ba su horo na mako 16 kafin su koma ga danginsu.

Kwamandan Rundunar Tsaro ta Operation Safe Corridor, Manjo Janar BM Shafa, ya bayyana wa tubabbun cewa an kawo su sansanin ne saboda gwamnati ta ga dacewar hakan saboda a dawo da su cikin hankalinsu su amfani al’ummarsu nan gaba.

Manjo Janar BM Shafa, ya yi kira gare su cewa su yi biyayya kan tsarin da aka shimfida da kuma bin ka’idojin sansanin domin su amfana da abin da za a koya musu.

Kwamandan da ayarinsa sun duba wurin da aka ware musammam don cin abinci sannan ya wuce dakunan kwanansu da kowane yake da gado sama da kasa da bargon rufa da gidan sauro da sabulan wanka da na wanki da sauran kayayyakin da suke bukata.

Kwamandan ya nuna farin cikinsa kan bayanin da ya samu game da abin da ya faru da mutum shida na farko da aka kai sansanin, kuma an nuna masa wata babbar gonar shinkafa da ta gyada da suka noma wadda wadansu daga cikin wadanda suka zo yanzu ne za su karasa aikinta.

Sansanin yana da rijiyar bohul da ake sarrafa ruwan leda ga tubabbun, kuma za a yi amfani da hakan wajen koya musu yadda ake yin ruwan ledar domin idan suka koma ga ’yan uwansu ya zama suna da sana’o’in da suke yi da za su kawar da hankalinsu daga aikata ta’addanci nan gaba.

Daya daga cikin tubabbun ’yan Boko Haram din mai suna Muhammadu Saleh, ya yi wa ’yan jarida bayani kan yadda suka ga inda aka kawo su, inda ya ce ashe sun jima suna shan wahala a daji kuma da sun san haka ne da tuni sun ajiye makamai sun mika wuya.

Muhammadu Saleh, ya ce suna gode wa Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojin kan kula da su tun daga lokacin da suka bar daji har zuwa lokacin da ake kokarin farfado musu da tunaninsu.

Galibin wadanda suka mika wuyan sun fito ne daga Gwoza wadanda ga alama yunwa ta galabaita su.

Manjo Janar BM Shafa, ya yi alkawarin cewa a lokacin da suke samun horon za a yi kokari a samu bayanin inda iyalansu suke domin a sada su da su bayan sun kammala samun horon.