Kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da harin tagwayen bama-bamai da ya kashe fiye da mutum 80 a wurin taron tunawa da babban kwamandan sojin Iran, Qassem Soleimani wanda jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a Iraqi a shekarar 2020.
IS ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da wallafa a shafin Telegram.
A cewar kungiyar, mayakanta ne suka tayar da bama-baman da suka yi damara da su a cikin dandazon jama’ar da suka hallara a makabartar da aka binne Soleimani da ke birnin Kerman a ranar Laraba.
- Faransa ta daure dan wasan Algeria kan goyon bayan Gaza
- An samu wanda ya fi Dangote kuɗi a Afirka — Forbes
Bayanai sun ce agwayen hare-haren sun kuma raunata mutane 284 da suka hada da mata da kananan yara.
Za mu yi zazzafar ramuwa kan wadanda suka kai harin ta hanyar amfani da sojojin Soleimani, inji Mohammad Mokhber, mataimaki na farko na shugaban kasar Iran.
Tun da farko, wata majiya ta shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Gwamnatin Kasar IRNA cewa, wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din farko a wurin taron tunawa da Soleimani wanda aka kashe shekaru hudu da suka gabata.
Majiyar ta ce, ga alama shi ma bam na biyu ya tashi ne bayan wani dan kunar bakin waken ya sake tayar da shi.
Tuni Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tur da wanna harin da ya bayyana a matsayin na matsoratan ’yan ta’adda a Kerman, yana mai mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma gwamnatin kasar.
Kafar talabiji ta kasar ta nuna hotunan dandazon Iraniyawa a sassan biranen kasar suna rera wake-waken, inda suke cewa “mutuwa ta tabbata ga Isra’ila”. “Mutuwa ta tabbata ga Amurka.”
Hukumomin Iran sun bukaci gudanar da gagarumar zanga-zanga a kasar a wannan Juma’ar, lokacin da za a yi jana’izar mutanen da suka mutu a harin tagwayen bama-baman.
Jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya yi alkwarin daukar fansa mai tsanani kan tagwayen hare-haren.
Khamenei ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin a ranar Laraba.
Jagoran addinin ya ce ”Muggan makiyan al’ummar Iran sun sake haddasa wani bala’i tare da kisan gilla ga al’ummar Kerman.”
“Da yardar Allah za mu mayar da martani kan wannan bala’in da aka jefa al’ummarmu.”
A ranar Alhamis ministan harkokin cikin gidan Iran, Ahmad Vahidia, ya rage adadin wadanda suka rasu a harin zuwa 84, wanda da farko hukumomi suka ce adadin ya kai 103.
Shugaban hukumar agajin gaggawar Iran, Jafar Miadfar, ya ce da farko an kirga wasu gawarwaki sama da sau daya, saboda tarwatsewar da suka yi, kafin daga baya a gano hakan.
Harin shi ne mafi muni da aka kai cikin Iran a tsawon shekaru 45 a tarihin kasar ta Jamhuriyar Islama.