Rundunar Sojin Najeriya, ta bayyana cewa bama-baman da ‘yan ta’addan Lakurawa suka birne a ƙauyukan da sojojin suka kai hari ne suka haddasa mutuwar mutanen garin, ba harin da sojojin suka kai ba.
Wannna na cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar, wacce Manjo Janar Edward Buba, daraktan yaɗa labaranta ya sanya wa hannu.
- Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa
- Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya
Rundunar ta ce sojojin ba su kashe mutanen ƙauyukan ba.
Manjo Janar Buba, ya bayyana cewa kafin sojojin su kai farmaki yankin, sai da suka yi dogon bincike, ta hanyar tattara bayanan sirri.
Bayan samun tabbacin cewa Lakurawa ne suke kai hare-hare da amfani da ƙauyen a matsayin mafaka, sai suka ɗauki matakin kai farmaki.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Laraba ne, jiragen saman sojin Najeriya suka kai hari wasu ƙauyuka guda biyu da ke Ƙaramar hukumar Silame, Jihar Sakkwato.
Harin dai ya yi sanadin mutuwar wasu mutum 10, tare da jikkata wasu.
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya bayyana cewa harin da sojojin suka kai ya faru ne bisa kuskure, kuma hakan ya jawo mutuwar mutum 10.