Fitaccen malamin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana irin matan da ya ce bai kamata mazajensu su yi musu kishiya ba.
Malamin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da karatu a majalisinsa da ke Kaduna.
- Majalisun jihohi da suke amfani da Hausa yayin muhawara
- Zulum ya fatattaki kungiyar da aka gano tana ‘koya harbi’ a otal daga Borno
A cewarsa, bai kamata mutum ya auri mace sama da daya ba kawai saboda addini ya ba shi dama, matukar ya san ba shi da sukunin rike su, ko kuma darajar matar da ya fara aure ta fi tashi.
Malamin ya kwatanta kara aure ga wasu mazajen da sayen motar da ta fi karfin samun mutum, yana mai cewa dole zai sha wahala sosai.
Ya ce, “Mutum bai kai ya hada mata ba amma ya ce zai yi, ko dai don kudi ko kuma darajar irin matan da yake son ya hada, alhali akwai inda zai je ya auri hudu, kuma dukkansu suna murna.
“Amma akwai inda komai kudinka ba za ka iya yi ba sai daya. Saboda irin wacce ka aura. Saboda haka ba kowace irin mace za ka aura ka ce za ka lafta mata ksihiya ba. Kawai da an zo ka ce Fankihu ma daba lakum… komai da matsayinsa.
“Ko Manzon Allah (S.A.W) da yana tare da Khadija yana da wahala ya kara mata kishiya don girmanta da sharafinta da kuma matsayinta a wurinsa. Amma lokacin da Allah Ya karbi ranta sai ya kara wasu.
“Kazalika Aliyu Bn Abi Dalib (R.A) da Annabi (S.A.W) ya aura masa diyarsa (Fatima) sai ya zo yana son ya auri diyar Abu-Jahal, sai Annabin da kansa ya hana shi, kuma bai mata kishiya ba sai da ta rasu saboda darajarta.
“To haka abin yake, ba za a taimaka maka ba sannan ka ce za ka yi kishiya, ko a rage maka sadaki, ko a ba ka gida, sannan ka ce za ka yi kishiya. Ba kai ba kishiya, sai dai in ta mutu.
“Akwai waliyyai na miji da na mata, in za a yi aure kamata ya yi a tsaya a ga sun dace ko ba su dace ba? Ba wai kawai so za a duba ba. Saboda zama ne na dindindin kuma na tarbiyyar al’umma. Kamata ya yi kowa ya dauki abin da ya dace da shi,” inji shehin Malamin.