✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kona ɗan kishiyarta da dutsen guga a kan N200

Ta ce ta yi hakan ne domin ta nuna masa kuskuren shi

Wata mata ta kona dan kishiyarta ta hanyar amfani da dutsen guga saboda Naira 200 a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu.

Matar, mai suna Mary Ita Edet, wacce ke auren wani mutum mai suna Offiong ta azabtar da dan goyon nata ne mai suna Daniel Offiong ta hanyar kona masa baya da dutsen guga.

Aminiya ta garzaya unguwar da lamarin ya faru, inda ta ji ta bakin uwargida Mary Ita Edet game da zargin da ake yi mata, inda ta ce, “Yaron sam ba ya jin magana. A duk lokacin da ya ga na ajiye kudi sai ya faki idona ya zara.

“A wannan karon sai na kirga kudina na ajiye, kafin na dawo sai na ga an zare Naira 200 cikin kudin.

“Abin ya bakanta min rai, shi ya sa na sanya dutsen guga a wuta da ya yi zafi na kamashi na rika goga masa a bayanshi sa domin ya ji zafi ya san abin da ya yi kuskure ne bai kyauta ba,”in ji matar.

Da wakilinmu ya tambaye ta ko ta yi nadamar abin da ta aikata sai ta ce, “Bacin rai ne, sai daga baya ne na gane cewar na yi kuskure.”

Yayin da ta samu labarin faruwar lamarin, Kwamishina Mai kula da walwalar jama’a ta jihar, Dokta Helen Isamoh Egodo, ta ce za ta ziyarci gidan tag a halin da ake ciki.

Da muka tuntube ta game da lamarin, ta ce ofishinta ba zai taba yarda da irin wannan hali na rashin imani ba, kuma matar za ta fuskanci hukunci.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Irene Ugbo, inda ya ce ba su da masaniya kuma galibi idan irin haka ta faru, mutane ba su cika kai wa jami’ansu rahoto ba.