Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Hausawa kan ce, kishi kumallon mata. Wannan ce ta sa muka kawo bayanai a kan irin nau’in kishin da a addinance ya halalta tsakanin kishiyoyi da kuma wanda ya dace maigida ya yi a kan matansa. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya zam ya amfanar da su, amin.
Ghirah: Shi ne irin kishin da ake son magidanta maza da ma wadanda ba su riga sun zama magidanta ba su kasance sun mallake shi, shi ne irin wanda sahabban Manzon Allah (SAW) su ke da shi.
Wato maigida ya kasance yana kishin matarsa sosai ta yadda yana jin haushi da bacin rai kwarai in ya gan ta tare da wani mutum wanda ba muharraminta ba, a ko ma wane irin yanayi ne, ya ji yana kishin bayyanar adonta komai kankantarsa ga wasu mazan da ba muharramanta ba, kuma sannan ya rika dagewa da tsarewa don ganin cewa irin wadannan abubuwa kwata-kwata ba su faru ba.
Irin wannan kishi ana son har kanne da yayye da mahaifa mata a rika yi masu shi, kuma ana kiyaye su ana tsare su daga afkuwar haka. Haka kuma yana daga cikin dabi’o’in da ake son Musulmin kirki ya kasance ya mallaka wato kishin duk wata mace Musulma, ta hanyar jin zafi in aka keta mutuncinta da kyamar bayyanar adonta ga wasu wadanda ba muharramanta ba.
In muka lura da abubuwan da suke faruwa a cikin gidajenmu da titunanmu a wannan zamani, za mu ga cewa irin wannan kyakyawan kishi na Ghira ya yi karanci sosai a cikin al’umma. Dubi yadda maza ke barin matansu suna fita cikin kwalliya da ado da yadda suke barin su suna hawa abin hawan da ke sa bayyanar da babban bangare daga tsiraicinsu da yadda suke kyale su yi tafiya mai nisa ba tare da wani muharrami ba da yadda suke barin matansu na zama da mazan da ba muharramansu ba a cikin gidajensu.
Tun daga ’yan uwa da kannen miji da abokan miji, masu aikin gida da makwabta da hakan har ya zama al’ada, ba maganar rufe jiki ko boye ado duk lokacin da irin wadannan suka shigo cikin gidan, sai a zauna a yi magana mai tsawo da su, wani sa’in har da wasa da dariya, ba tare da cikakken hijabi ba, kuma Mijin yana kallo, amma bai jin kyamar abin balle har ya hana.
Haka kuma, ba ta abin da suke yi a kafafen sada zumunta. Sannan matan ma ba su kishin kansu daga bayyanar da suffarsu ga wasu mazajen da ba muharramansu ba, balle har su yi kokarin taya mazajensu kishin ghira ta hanyar suturce kansu da boye kwalliyarsu domin mazajensu kawai, wasu ma hankalinsu bai kwantawa har sai sun bayyanar da adonsu da kirar jikinsu da kwalliyarsu ga duniya, ba su san cewa irin yin hakan na tsananin rage masu armashi, da daraja da kima ba.
Alkur’ani Mai girma ya yi umarni ga maza cewa, duk lokacin da ganawa ta zama dole a tsakaninsu da matan da ba muharramansu ba, to su yi ta da hijabi a tsakani, wato ya kasance akwai wani abin da ya katange idanuwansu daga ganin juna.
Sannan Annabi (SAW) ya yi umarni ga maza cewa: “Ku kiyayi shiga wajen mata (yayin da suke cikin gidajensu).” Sai wani sahabi (RA) daga cikin Mutanen Madina ya ce “Ya Manzon Allah har kanin miji ma?” Sai Annabi (SAW) ya ba shi amsa da cewa ai kanin miji shi mutuwa ne ma gaba daya! Wato shi ne kankat wajen bala’in da ke tattare da kasantuwar mace da duk wani namijin da ba muharraminta ba.
Kuma mu lura wannan hukunci ya shafi har kanwar mata a tsakaninta da mijin yayarta, in dai ta balaga to dole ta rufe jikinta koyaushe a gaban mijin yayarta.
To an ce kanen miji mutuwa ne ina kuma ga abokan miji, makwabta da ’yan aiki? Da miliyoyin mazan da ba a san su ba, amma zamani ya kawo ana hira da su a yi wasa da dariya ta hanyoyin sadarwa daban-daban? Da fatar Allah Ya ba mu ikon farfado da kishinmu na Ghira, da gyara wannan kazantar da ta yawaita cikin gidajenmu, amin.
Dangane da mata, irin kishi mai amfanin da ake son su yi a tsakaninsu da kishiyoyinsu, shi ne irin wanda Iyayen Muminai (Radiyallahu Anhunna) suka yi a gidan Annabi (SAW), wato kishi mai tsabta wanda babu cutarwa ko ketare haddi a cikinsa.
Yana da kyau kishiyoyin juna su yi kishi ta hanyar yin rige-rige wajen kyautata wa mijinsu, ta hanyar yin kyawawan abubuwan da za su soyantar da su ga mijin nasu, amma da sharadin in dai ba za su aikata wani abu da zai cutar da abokiyar zama ko maigidansu ba.
Ba haramun ba ne jin haushin abokiyar zama saboda wani dalili, wannan shi ne kishi. Sai dai haramun ne yin duk wani aiki a dalilin jin kishin nan da zai cutar da abokiyar zama ko miji.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba inshaAllah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.