Iran ta zargi Isra’ila da kai mata hari da jirage marasa matuka a wata masana’antar soji.
Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya shaida mata cewa bincikensu ya gano cewa gwamnatin Isra’ila ce ta kai harin a lardin Isfahan.
- Harin Masallaci: ‘Dan sanda’ ne ya kashe mutum 101 da bom a Pakistan
- Kwankwaso bai gana da Atiku ba, ba zai goyi bayan kowa ba —NNPP
A wasikarsa ga Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kuma zargin kalaman barazanar jami’an gwamnatin Isra’ila na kai hari kan kadarorin Iran.
Sai dai, Iravani bai yi karin bayani kan zargin ba, amma yana “Bukatar Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ya la’anci wannan abin kyamar da Isara’ila ta aikata.
“Sannan ta tilasta mata bin dokokin kasa da kasa da kuma shirye-shiryenta masu hadari a yankin.”
An shafe shekaru ana yakin bayan fage tsakanin Isra’ila da Iran wadda ke zargi da kai hare-haren rusa shirinta na nukiliya, da hadin bakin Amurka.