✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta zargi Amurka da kitsa yaki a duniya

Iran ta zargi Amurka kan zama kanwa uwar-gami a dukkanin yake-yaken da ke faruwa a duniya. A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na…

Iran ta zargi Amurka kan zama kanwa uwar-gami a dukkanin yake-yaken da ke faruwa a duniya.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Mista Javad Zarif, ya ce Amurka ce kan gaba a duniya wajen sayar da makamai da kashe kudi a kan al’amuran soji.

Ya kuma ce Amurkar ce ke rura wutar yake-yake da kitsa fitintinu a kasashen duniya domin samun riba daga rashin zaman lafiya.

Mista Zarif ya kara da cewa: “Duk da hakan, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya damu da Iran matuka – wacce ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Amurka ta fuskar cinikin makamai har zuwa shekarar 1979,

“Hakan ya sa Amurkar ke baza makamai ko ina a duniya,’ˋ inji Mista Zarif, wanda ya yi amfani da wani hoton bidiyo da ke nuna yawan makaman da Amurkar ta fita tun daga

Ga alama dai Mista Zarif na mayar da martani ne ga wani zargin da Mike Pompeo ya yi a nasa shafin na Twitter cewa ‘yan dabar Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela sun sato tan tara na zinare sun aike wa Iran.

“Manyan barayin duniya sun hada hannu da manyan masu kitsa ta’addanci a duniya. Wadanda suka fi kowa asara su ne al’ummomin Venezuela da Iran”, inji Mista Pompeo.

Iran da Amurka  dai ba sa ga maciji da juna tun bayan juyin juya halin shekarar 1979 lokacin da Iran din ta koma jamhuriyar Musulunci.