Iran ta kama mutane shida kan zargin kasancewa ’yan leken asiri ga Isra’ila.
Rahotannin kafofin watsa labarai na ƙasar Iran sun nuna cewa mutanen shida suna leken asiri ne ga hukumar leken asiri ta Isra’ila, Mossad, kuma an kama su ne a lardin Hamadan da ke yammacin kasar.
Ali Akbar Karimpour, wani jami’in Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa an kama “‘yan cin amanar ƙasar,” ne a garuruwan Hamadan, Razan, da Nahavand a cikin lardin.
Ya kara da cewa ana zargin su da gudanar da ayyukan ta intanet da nufin haifar da tashin hankalin jama’a, ɓata sunan gwamnatin Iran, da kuma gurɓata sunanta.”
Iran ta kama mutane da dama kuma ta kashe wasu da dama saboda leƙen asiri ga Isra’ila tun bayan fara yaƙinta da Isra’ila.