✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila

Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ne ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya.

Iran ta kai hari a kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad) kamar yadda kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran suka ruwaito a ranar Talata.

Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ba da rahoton cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya.

Tasnim ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda hedikwatar ta Mossad ke ci da wutan ne bayan harin makamai masu linzami ne da Iran ta kai mata.

Kafar yaɗa labarai ta Tehran Times ta ruwaito cewa hare-haren na IRGC sun ƙona wani ɓangare na cibiyar Aman, wanda wani ɓangare ne na ginin hukumar leƙen asirin asirin sojin Isra’ila ta Aman, da ke Glilot.

Kawo yanzu dai ba a iya tantance sahihancin wannan iƙirarin na Iran ba daga kafofin yaɗa labarai da ke aiki a yankin; kuma hukumomin Isra’ila ba su ce uffan a kai ba.

A cewar hukumar kare haƙƙin ɗan’Adam a Iran (HRANA), fararen hula 224 ne suka mutu, yayin da 188 suka jikkata a hare-haren Isra’ila a ƙasar.

HRANA ta kuma bayyana cewa sojoji 109 ne suka mutu inda kuma 123 suka jikkata.