✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran da Saudiyya za su koma tattaunawar gaba-gadi

Alamu sun nuna kasashen Iran da Saudiyya za su koma tattaunawar gaba-gadi wanda Iraqi za ta karbi bakwancinsu nan ba da jimawa ba. Sabon Ministan…

Alamu sun nuna kasashen Iran da Saudiyya za su koma tattaunawar gaba-gadi wanda Iraqi za ta karbi bakwancinsu nan ba da jimawa ba.

Sabon Ministan Wajen Iran, Hossein Amirabdollahian, a wata hira da gidan talabijin din kasar a daren Talata ya ce ya yi magana da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud, a yayin taron kolin yankin da ya gudana a birnin Bagadaza ranar Asabar.

“Takwaran nawa ya ce suna jiran sabuwar gwamnatin Iran ta tsaya da kafafunta sannan sai mu koma ga batun tattaunawarmu da ita,” inji Amirabdollahian.

Kasashen biyu da ke zaman doya da manja sun fara tattaunawar sulhu a watan Afrilu a Bagadaza babban birnin Iraqi amma aka katse zaman har sai an Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya kafa gwamnati.

Majalisar Zartarwar Shugaba Raisi ta samu gagarumin goyon baya daga majalisar dokokin Iran kwanaki kadan gabanin taron kolin Bagadazan, wanda shi ne ziyarar aiki ta farko da Amirabdollahian ya gudanar a matsayin ministan harkokin wajen kasar.

Shi ma Jakadan Iran a Bagadaza ya tabbatar da cewa nan gaba kadan za a ci gaba da tattaunawa da jami’an Saudiyyar karo hudu.

“Iran ta ce ta shirya tsaf domin sulhun zaman lafiya sannan ta nemi agaji daga makwabtanta da sauran kasashen yankin,” inji Iraj Masjedi.

An yi tattaunawar ce da zimmar nema wa Iran goyon baya sannan ta kasance wata muhimmiyar alamar yunkurin kasashen yankin wajen rage tankiyar da ke faruwa a yankin Gulf

Karon farko ke nan cikin fiye da shekara biyar da manyan jami’an gwamnatocin Iran da Saudiyya ke zama a waje guda domin halartar taro daya.

Mahukunta a Riyadh da Tehran sun katse huldar jakadanci tsakaninsu tun farkon 2016 bayan wani gungun jama’a suka far wa ofishin jakadancin masarautar Saudiyyar a birnin Tehran bayan kisan wani babban malamin Shi’a a Saudiyyar.

Wutar tankiya tsakanin kasashen ta karu bayan Saudiyya ta ce za ta goyi bayan gangamin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na tsaurara matsin lamba kan Iran bayan Trump din ya yi gaban kansa wajen fitar da kasarsa daga Yarjejeniyar Nukiliyar 2015 da sauran manyan kasashen duniya.

A 2019, jami’an Amurka da Saudiyya sun zargi Iran da kai harin makami mai linzami da na kurman jirgi da aka kaddamar kan rijiyoyin man wanda ya sa Saudiyyar ta dan rage man da take fitarwa da wajen rabi na wani dan lokaci.