✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran da Saudiyya na daf da maido da huldar diflomasiyya

Rahotanni sun ce wakilan Iran sun isa birnin Jeddah na Saudiyya domin fara aiki.

Jakadun kasar Iran sun koma cikin Kungiyar Kasashen Musulmai (OIC) mai hedikwata a kasar Saudiyya, a matakin farko na maido da alaka a tsakanin jasashen biyu bayan sun katse huldar diflomasiyyarsu a shekarar 2016.

Rahotanni sun ce wakilan Iran sun isa birnin Jeddah na Saudiyya domin fara aiki a karkashin kungiyar ta kasashen
Musulmai.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce, wannan wani mataki ne da ke nuna cewa, jasashen biyu za su mayar da
jami’ansu a ofisoshin jakadancin kowace daga cikinsu.

Kungiyar OIC ta ce, ayarin Iran xin ya isa birnin Jeddah amma kawo yanzu babu wani taro da suka halarta, kamar yadda wani jami’i a Kungiyar Kasashen Musulmai ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP).

Ana sa ran Jakadun Tehran su halarci wani karamin taron ministoci a jibi Lahadi kamar yadda jami’in ya yi karin haske.

Iran wadda take da mafi yawan mabiya akidar Shi’a da Saudiyya wadda ke da mafi yawan mabiya akidar Sunni, dukkansu mambobi ne a Kungiyar Musulmai mai kunshe da kasashe 57.

Kasashen biyu da ba sa ga-maciji da juna sun gudanar da tattaunawa sau hudu a Iraqi daga watan Afrilun bara da zimmar maido da alaka a tsakaninsu.