Kungiyar IPOB ta sake harbe jami’an ’yan sanda biyu ta kuma kona ofishin ’yan sanda a Jihar Abia.
A safiyar Litinin IPOB ta kai harin a ofishin ’yan sanda da ke cikin babbar kasuwar Ubakala a Karamar Hukumar Umuahia ta Kudu ta jihar.
- Musulmai ’yan kabilar Ibo na komawa Arewa saboda tsangwama
- Budurwa ta fada rijiya a Kano
- Kano: An bude makarantun da aka rufe saboda matsalar tsaro
Wani jami’in dan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa bayan samun labarin yiwuwar kawo harin, an umarci jami’an da ke ofishin cewa su tsaurara matakan tsaro ko su rufe ofishin, amma ba su yi ba.
Harin shi ne na karshe da ake zargin kungiyar IPOB ta kai wa cibiyoyin gwamnati a yankin Kudu-maso-Gabashin Najeriya.
Kafin shi, ’yan bindiga sun kai wa ofishin ’yan sanda da ke Enugu hari, kuma kafin shi sun kai hari da roka inda suka kona ofishin ’yan sanda na Bende a Jihar Abia.
An kai harin Bende ne jim kadan bayan makamacinsa a ofishin ’yan sanda na Uzuakoli wanda aka yi amfani da makamin roka.
A makon jiya, an kai wa ofishin ’yan sanda da ke Kasuwar Ubani hari, bayan an kona ofishin Hukumar Zabe ta Kasa a Karamar Hukumar Ohafia a makon shekaranjiya.