Bayan kimanin shekaru 11, kungiyar Inter Milan ta samu nasarar lashe gasar Serie A ta bana.
Kungiyar ta samu wannen nasara ne bayan ta bayar da tazarar maki 13 yayin da rage wasanni hudu a kammala gasar.
- Gidauniya ta raba wa Marayu 400 kayan Sallah a Ajingi
- Likitan da ya ba da gudunmawar kashe Osama ya nemi a sake shi
Nasarar da Inter ta yi na zuwa ne sakamakon kunnen doki da Atalanta da ke ta biyu a teburin ta yi da Sassuolu a ranar Lahadi.
Inter Milan ta lashe gasar ce a karkashin jagorancin mai horas da ’yan wasanta, Antonio Conte, wanda yake shekara ta biyu wajen ragamar kungiyar.
Kofin Serie A da Inter Milan ta lashe shi ne kofi na farko da kungiyar ta ci tun bayan lokacin da Jose Mourinho ya daukar mata gasar da kofin Zakarun Turai a shekarar 2010.
Tun Asabar din da ta gabata ce yaran Antonio suka kyalla idanunsu a kan kofin Serie A na bana, bayan sun lallasa Crotone a haduwar da suka yi ina aka tashi 2-0.
A bana dai Inter ta ciki wasanni 25, sai kuma canjasar biyar da kuma shan kashi da ta yi sau biyu cikin duk wasannin gasar Serie A ta bana.
A yanzu Inter Milan da ake yi wa lakabai da Nerazzurri ta shiga murnar lashe gasar Serie A cikon ta 19 a tarihin kungiyar.