✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Instagram: Hotunan Davido Da Masoyiyarsa Ne Mafi Farin Jini a Najeriya

Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wato Davido, ya sake kafa tarihi a Najeriya, bayan wallafa hotunansa tare da masoyiyarsa Chioma a ranar Litinin, inda ya…

Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wato Davido, ya sake kafa tarihi a Najeriya, bayan wallafa hotunansa tare da masoyiyarsa Chioma a ranar Litinin, inda ya zama hoton da ya fi kowanne farin jini a kafar Instagram a kasar.

Cikin hotunan da masoyan suka dauka gabanin gudanar da wasansa na a bikin rufe Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, an ga masoyiyar tasa Chioma na dandashe shi da kwalliya cikin yanayi na soyayya.

Hoton da ya samu ‘Like’ miliyan 1.7, shi ne na farko da ya wallafa a shafin nasa, tun bayan rasuwar dansa a watan Oktoba.

Davido ya gudanar da wasan ne a filin wasa na Lusail da ke Qatar, tare da sauran manyan mawaka daga sassan duniya daban-daban irinsu Aisha, Ozuna da GIMS.