Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai Kasar Qatar.
Jirgin shugaban kasa, ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja da misalin karfe 7 na yammacin ranar Litinin.
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya za ta fara rabon hatsi
- HOTUNA: Yadda al’ummar Nasarawa ke fama da rashin ruwan sha
Wannan dai ita ce tafiya ta 12 da shugaban kasar ya yi tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a watan Mayun 2023.
Tinubu ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Sauran sun hadar da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Darakta Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje, Yusuf Bichi, da dai sauransu.
A ranar farko ta ziyararsa, Tinubu, ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na kasar Qatar, inda ya jaddada muhimmancin adana kayan tarihi.
Tinubu tare da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniya guda bakwai a tsakanin kasashen biyu, bayan ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban kasar da ke Doha.
Sun sanya hannu kan hadin gwiwa a fagen ilimi; ka’idojin daukar ma’aikata tare da gwamnatin Qatar; kafa majalisar hada-hadar kasuwanci tsakanin kungiyar ’yan kasuwa da masana’antu ta Qatar da kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu da ma’adinai da noma ta Najeriya; baya ga yarjejeniyar hadin gwiwa a fagen matasa da wasanni.
Sauran sun hada da hadin gwiwa a fannin yawon bude ido da harkokin kasuwanci, da kuma yarjejeniya kan yaki da fataucin miyagun kwayoyi.
Shugabannin kasashen biyu, sun jadadda aniyarsu na ci gaba da kulla kawance don amfaninsu.