Wani jirgin sama na mallakin kamfanin Dana Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Kamfanin Dana Air, ya ce jirgin nasa kirar kirar Boeing 737 mai lamba 5N DNA, yi saukar gaggawan ne bayan matukinsa ya lura cewa injinsa ya samu matsala a sararin samaniya.
- Yadda hana tukin Adaidata Sahu da daddare zai shafi rayuwarmu — Kanawa
- Kotu ta sa ranar fara sauraron karar da Abduljabbar ya shigar da gwamnatin Kano
“Matukin jirgin ne ya yi maza ya bayyana wa fasinjoji halin da ake ciki, tare da sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja lafiya da misalin karfe 2:52 na rana”, acewar sanarwar.
“Mun bayyaa wa Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya komai, kuma muna neman afuwar fasinjojin da muka dauko.
“Muna kuma tabbatar musu da cewa kamfaninmu zai ci gaba da aiki cikin kwarewa kamar yadda aka san shi a baya,” inji sanarwar da kamfanin ya fitar.