Hukumar Gasar Firimiyar Ingila ta sanar da cewa kungiyoyin ta ba za su kyale ’yan wasansu halartar wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya da kasashensu za su buga ba a watan gobe.
Matakin dai ya shafi ’yan wasan da kasashensu ke cikin wadanda Birtaniya ta bayyana a matsayin masu hatsari saboda fama da annobar Coronavirus.
- Ba za mu dauki Ronaldo ba a bazarar nan —City
- Fadar Shugaban Kasa ta dora alhakin kashe-kashe kan gwamnan Benuwai
Bayan wannan sanarwar da Firimiyar Ingila ta fitar, mahukunta Gasar La Liga ta Spain ta ce za ta goyi bayan kungiyoyin da suka yanke shawarar kin bai wa ’yan wasansu izinin zuwa kasashen da aka sanya cikin jerin masu hatsari saboda Coronavirus.
Hukumomin Kwallon Kafar sun ce za su yi la’akari da cewa ’yan wasan da suka yi balaguro zuwa kasashen masu fama da annobar Corona, dole ne su bi ka’idojin kebe kansu bayan komawa Turai.
Sai dai idan hakan ta kasance, babu shakka wannan mataki zai sanya ’yan wasan rasa samun buga wa kungiyoyinsu wasanni yayin da suke killace.
A halin yanzu, wannan mataki na nufin kungiyoyi irinsu Liverpool ba za ta saki taurarinta da suka hada da Mohamed Salah ba, da Fabinho, Roberto Firmino da kuma Alisson Becker don wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya na Brazil da kuma Masar.
Kamar ’yan wasan na Liverpool, taurarin Manchester City ciki har da Ederson da Gabriel Jesus ma ba za su samu damar buga wa Brazil wasannin neman gurbin cin Kofin Duniya ba.
A takaice dai a Firimiyar Ingila kadai, kusan ’yan wasa 60 ba za su samu damar zuwa kasashensu don haska musu a wasannin sharar fagen gasar cin Kofin Duniya da za su yi ba a wata mai kamawa.