Alif silin nunin kasan madambacin nunin kasa
An kafa hukumar tushintasa
Asusun dukiya ya san makamar masa
’Yan damfara kar sui kissa
Ana bikin hawa kimar benen bisa
Hada-hadar lallaga sisi
A Haurubja Ko Jihar Logar-sisi
Hukuma ta bayar da lasisi
Asusun da bakarfanfanarasi
Akwai shakku da wasi-wasi
Wasu sun sha zama
Wasu na lasar maskin madin zuma
Wa-ka-ci-ka-tashin ’yan zalama
Wadanda suka tumurmushe al’umma
Wafciyar sukuwar ingarma
Ja-gaban wannan lamari
Shi ne Umari
Da ya jajirce kan aiki nagari
Kariyar asusun ajiyar mutan gari
Muna nai maka barka da kokari
Ka san akwai sasari
Miyagu sai an sa su mari
Kumatunsu na ta kumburi
Sun washe mai tumaturi
Masu kayan miya a dai yi jimiri
Inda-indarin dararo
In’inar karo-karo
Turnukun tasgaro
Gurmuzun gwagwiyar goriyar goro
Kugin kankareren karo
Dabarbarun dunguren duguro
In yidirar dirkowar daro
Kwararar kudi kwararo-kwararo
Wasu daure da kyauro
Sun warwatse sun zazzaro
Ruwan kudi
Rajinrurin kaudi
Ragargazar radadi
Rugumniyar rudi
Rarumar ridi
Shekaru kofar hancin zagaye
Asusu-asusun ajiye-ajiye
Ana ta kokari a kiyaye
Asara a tarairaye
Sha’anin shan-kan shakiyai yai kaye
Indai da sisi
Kwabo da taro ba wasi-wasi
’Yan kasuwa asin-da-asin asi
Daga birnin Dabo zuwa Kumasi
Hada-hadar dukiya ana bin bahasi
Ka da a nunke al’umma a baibai
Ana ta kwashe musu kwabbai
Turmin dakan dukiya ya haifar da tabbai
Motsin mutsuttsuke matsabbai
Mutane sun karke da jawabai
Asusun karfin giwa
Ajiya na wulkitawa
Mai dukiya na fantamawa
Ma’aikata na shakatawa
Rabon riba na dada hauhawa
Mabudin dutse
Fatara an kwamtse
Talalar talauci ta katse
Masu dandatsa ban da kutse
Hada-hada ake a kimtse
Asasin assasa as-as
Mai tulin kudi cunkus
Mai dukiya kan kari kan ji dumus
’Yan kwadago a lumanar lumus
Ba rade-raden gulmar kus-kus
An dai kiyaye asara
Da toshe kafar algarara
Aka kuma kara
Da daurin damara
Shige da ficen kudi ba jira
Burgamen bajintar Santali
Tarin dukiya tuli-tuli
Aiki ake da natson hankali
Ba a fatali
Ko kwasar kudi ai shagali
Uba mai tarairayar dukiyar ’ya’ya
Asusun ka ya biya awalajar kaya
Masu dako sun san an biya
Matsabbai sun yi zirya
Hukumar Inda-sisina ta bibiya
Kakkarfan Ingarma
Gadon bayansa kudi sui magama
An dai hana karma-karma
Ko na kudin cizo da kuma
A dai kiyayi dama-dama
Dakon dakon dukiya
Dakin dakan dakakkiya
Daurin damarar dawainiya
Daure-dauren daddake dirkaniya
Dogewar doke danniya
Inda-sisi
Kar ai kwafsi
A kare taro da sisi
Kowa ya samu natson lasisi
Kar a zo ana laluben asi
Hukumar hada-hadar hantsewar hatsin hantsin hasafin kariyar asusu-asusun ajiyar al’umma a kasar Haurobiya ta yi bikin cikarta shekaru kofar hanci da zagaye da kafuwa, inda ake ta murna kan irin wannan kimar matsayi da ta kai. Wannan sha’anin biki ya wakana ne tare da gunduma-gunduman bakin da aka gayyato daga ciki da wajen kasar nan. Kusan kowa sai sambarka ya yi wa wannan hukuma, musamman Malam Umari da ke jan ragamar babban al’amari, wajen kare matsabban mutanen gari, wanda aka yi masa barka da kokari, musamman yadda ya jajirce da kwazon aiki nagari.
Ni kuwa na fasko cewa, a wajen bayar da kariyar kange kasassabar assasa asarar asusu-asusun ajiye-ajiyen al’umma, wannan hukuma ta Inda-sisi mai bin bahasin tarin taro da sisi tana da jan aiki a gabanta, musamman in an yi la’akari da yadda a ’yan shekarun nan ’YAN DAMFARAR DAMUN-FURA, suka ci kolonsu babu babbaka, har ta kai ga an tsuwurwurta turka-turkar takun sakar TURMIN DAKAN HAURO da MOTSIN MUTSUTTSUKE MATSABBAI, inda Mai-burodi ya yi bidiri birede da dukiyar Haurobiyawa, inda daga bisani ya garkame gambu da jimamin jama’a. A daidai lokacin da Haurobiyawa ke fama da tataburzar tarnakin tafkar Mai-burodi, da aka koka wa Malam Umari, cewa ya yi, su dai a Hukumar Inda-sisi du’a’in rokon Mai-duka kawai za su yi wa al’umma, don tuni suka ja na-zomon al’umma kan lallai su kiyayi masu walwalin waliyon walankeluwar wulkice-wulkicen wulwulawar wa-ka-ci-ka-tashin watayawar walwalar wala-wala. Kuma da barewa ta arce da damin matsabban al’umma a zamanin mulkin Baba-ojo mai gonakin Otawa, shin wane namijin yunkuri wannan hukuma ta tabuka don rage radadin asara?
Uwa-uba, wannan Hukuma ta Inda-sisina tana sane da cewa an antayo damin matsabban garkuwar gagara-kuwwa da matsabban damfarar damun-fura a asusu-asusun ajiyar da ke fadin Haurobiya, shin ko ba za ta iya bai wa ’yan kasa kariya ba ne?
Akwai azargagiyar zizarar ziryar zarge-zargen cewa, hadin bakunan ’yan kwadagon da ke laluben kadago a asusu-asusun ajiya na da hannu dumu-dumu wajen tafka ta’asa, shin ko Inda-sisi ta taba bin kadin lamarin?
Al’amuran dai da ke cutar da hada-hadar Hauro sanannu ne, don haka sai a kauce wa Inda-indar indararo ko dirar dirkowar darewar daro da kwararar da kudi a kwararo-kwararo, musamman wadanda ke daure a kyauro gudun kada su warwatse su zazzaro. Domin wadansu za su baza laftun labarai cewa, ana ta ruguntsumin ruwan kudi, tare da rajin rurin kaudi mai ratattakar rangajin ragargazar radadi a rugumniyar rudin rarumar ridi.
Kuma shekaru kofar hanci da zagaye na Hukumar Inda-sisi asusu-asusun ajiye-ajiye na ta kokarin kiyaye asara a tattare, a tarairaye- tarairaye wajen sha’anin shan-kan shakiyai gudun kaye. Shi ke nan in dai da sisi, kwabo da taro ba wasi-wasi a tsakanin ’yan kasuwa masu tarin asi, wato daga birnin Dabo zuwa kasar Ghana a yi gane-gane a birnin Kumasi, wajen hada-hadar dukiya ana ta bin bahasi.
Abin taradaddi dai, shi ne, kada a nunke al’umma a baibai, har a kwashe musu kwabbai, tamkar dai yadda lamura suka wakana a dakan turmin dakan dukiya, wanda ya haifar da tabbai, aka zo aka karke a motsin mutsuttsuke matsabbai, har mutane suka karke da janjanin jawabai
Lallai akwai bukatar bai wa Haurobiyawa tabbacin cewa akwai lullumin lumanar luntsumar lumui-lumui lumus a tsakanin wannan hukuma da asusu-asusun ajiyar al’umma da suka hada da: Katuwar giwa da kakkarfan ingarma da Uba da Burgamen bajintar Santali da Asasin assa as-as da makamantansu. A yi ta fafutikar yaye duhun juhala don tabbatar da adala, gudun kwamacala, ta yadda za a yi ta hada-hada bisa ka’idojin doka, kada kowa ya koka. A kiyayi kidahumanci, a yi komai cikin mutunci, tare da kauce wa camamar ci-mu-cin cincirindon cin ca’ammas ko cuku-cukun cacumar cukubus da artabun aikin amso alkubus.
A dai yi hattara, a kauce wa LAFTUN LISSAFIN LIYAFAR LAIFUFFUKAN LUKUDIN LAKUME-LAKUMEN LAMUNI. Domin irin wannan ta’asar ke haifar wa harkokin hada-hadar tattalin tulin tuttule tulu, ai ta kwan-gaba, kwan-baya. Karshe dai a yi ta jefa azargagiyar zarge-zarge a inda ba su dace ba, har hakikanin wadanda suka tafka ta’asa a kwanon tasa su samu sarari su arce, ba wani ka-ce-na-ce.
Mu dai ’yan makarantar Dodorido mahayan shorido, muna matukar kyarar INDA-INDAR IN’INAR INDARARON INDA-SISI, amma muna matukar kaunar INGANTACCEN INGARMAN INDARARON INDA-SISI. Domin ta haka ne kawai za a bi kadin batan dabon taro da sisi, tare da bin bahasi kan kowace karfamfanar assasa asarar asi.
Matukar makekiyar hukumar tarairayar takure turka-turkar asarar ajiyar asusu na son ta ci gaba da karin shekaru masu albarka, sai ta himmatu ka’in-da-na’in wajen tunkude tarnakin tataburzar turka-turkar tauye hada-hadar hambudar handamar hautsinin hantsewar hatsin Haurobiyawa. Kai kodai so ake a karke da kafa kwatankwacin Hukumar AMAN-KUNU, wadda ta cefano asarar kamfanoni da asusu-asusun ajiya da suka durkushe ko samarin-kusu da ’yan matan jaba da gafiya suka yi musu murkusun muku-mukun makurar karkaf, inda suka wawushe komai-da-komai, har ma suka bi da maimai, ba tare da wata manufa takamaimai ba, amma har yanzu ba ta halarto da irin dimbin nasarorin da ta samu wajen juya asara ta zama gagarumar gwaggwabar riba ba?