A yayin gudanar da taron ’yan jarida na duniya karo na 67 da ya gudana a bara a Abuja a ranakun Alhamis 21 zuwa Asabar 23 ga Yuni, masana sun maida hankali ne wajen bayyanawa da fadakarwa dangane da muhimmancin samar da aikin jarida mai inganci, wanda zai taimaka wajen saita al’amuran shugabanci da samar da mulki mai adalci ga al’umma.
Haka kuma, kwararrun masana harkar jaridanci sun tattauna, sun yi bayanin irin kalubalen da aikin jarida ke fuskanta a wannan lokaci, musamman a sakamakon samuwar kafafen sadarwar sada zumunta na zamani.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya kasance babban bako a taron, ya bayyana muhimmancin da ke tattare da ingantaccen aikin jarida. Ya bayyana cewa: “Idan aka samu cewa labarun karya suke tasiri a al’umma, fiye da ingantattun labarun da ake samu ta hanyar bincike, to lallai ana bukatar ingantaccen aikin jarida. Haka kuma madamar ana bukatar tsira daga dukkan kalubalen rayuwa, to ana bukatar ingantatccen aikin jarida.” Wannan bayani ya kunshi a takaice faffadan abin da al’umma da gwamnati ke bukata daga aikin jarida. Abin nufi, ana bukatar ’yan jarida su jajirce wajen gudanar da aikinsu ta hanyar kwakkwaran bincike, wanda ta wannan hanya ce ake bankado sirrin hamshakan shugabannin al’umma, wanda haka kan saita su, su guji yin abin da bai dace ba a cikin al’umma. Haka kuma Buhari ya tabo illar da ke tunkarar al’umma a yanzu, wacce ita ce ta yaduwar labarun kanzon kurege.
Babban abin da ya haifar kuma yake azzara yaduwar labarun karya a cikin al’umma, shi ne samuwar kafafen sadarwa na zamani (Social Media), wanda ta hanyar intanet, an wayi gari mutanen da ba su da kwarewa ko ilimin aikin jarida suka zama ruwan dare, suke cin karensu ba babbaka a fagen jaridanci, fiye da ’yan jarida na ainahi. Ta hanyar intanet, labari ya zama mai saukin yadawa ta hanyar wayar hannu ko karamar kwamfuta ta hannu da sauransu, don haka babu mai tsayawa ya shirya rahoto mai inganci da bin ka’idar aikin jarida.
Domin ceto aikin jarida na ainahi daga fadawa garari, masana da suka tattauna a wannan taro sun ba da shawara ga gidajen jarida da su rika ware sashi na musamman, inda za a rika tantance labarun da ake samu ta intanet, domin kauce wa yada labarun karya. Babu shakka labarun karya na kassara aikin jarida kuma suna kawo faduwar darajar kowane gidan jarida da ya siffatu da wallafa labarun karya. Don haka, abu ne mai muhimmanci ga ’yan jarida da su tashi tsaye su gudanar da aikinsu yadda ya dace, ta hanyar bin ka’idojin aikin yadda ya kamata.
Haka kuma, wani al’amari da masana suka tattauna a yayin wannan babban taro na duniya, shi ne batun gudanar da gidan jarida, wanda a kullum sai kara wahala yake. A yau, masu gudanar da sana’ar jarida na fuskantar matsi sosai ta fuskar kudin gudanarwa, domin kuwa wasu gidajen jaridu da dama sun kasa gudanarwa, sun durkushe. Amma duk da haka, ya kamata gidajen jaridu su rungumi zamani, su fuskanci kalubalen ta hanyar sabbin kirkire-kirkire, yadda za su ci gaba da gudanarwa.
Aikin jarida yana da matukar muhimmanci, musamman wajen tafiyar da mulkin adalci, musamman ma irin na dimokuradiyya. Aiki ne da ke samar da ’yancin dan Adam da tabbatar da shi da kare shi. Haka kuma, yana taimakawa wajen gudanar kasuwanci da tsaro da dukkan al’amuran yau da kullum na al’umma. Don haka ya zama wajibi ga gwamnatoci da jami’an tsaro su kiyaye take hakkin ’yan jarida. A daina kama su da dakile aikinsu ba bisa doka ba, a daina kashe su saboda ta’addanci ne yin haka, musamman a yayin da suke gudanar da aikinsu na halal.