✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta tafka gagarumin magudi a zaben Kogi —Ajaka

Ajaka ya kare a matsayi na biyu da kuri'u 259,052 a zaben da aka gudanar ranar Asabar

Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a Kogi, Muritala Ajaka, ya caccaki Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kan yadda zaben gwamna ya gudana a jihar. 

Bayan hukumar ta ayyana Usman Ododo na Jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben da Ajaka ke neman kwace ragamar jihar daga jam’iyyar.

Dan takarar na SDP ya zargi jami’an INEC da aka aika jihar da yin magudin zabe inda ya kara da cewa “INEC ta ba mu kunya.”

A wata tattaunawa ranar Lahadi da gidan talabijin na Channels kan zaben gwamnan jihar, Ajaka ya ce, “Na gamsu cewa jami’an da aka tura jihar su suka shirya komai.

“Kafin a fara zaben, an riga an fitar da takardar sakamakon zaben a ko’ina a fadin Jihar Kogi ta Tsakiya.

“Tabbas mun rubuta musu kokenmu kuma muna da shaida. Abin takaici ne yadda wadannan abubuwan suka faru.

“Da mun san cewa daji za mu shiga, da mun yi masa shiri irin na shiga daji,” in ji Ajaka.

Ya ci gaba da cewa “Gwamnatin Tarayya ta yi nata bangaren kuma dole ne mu yi wa Shugaba Ahmed Bola Tinubu godiya. Ya samar da tsaro ga kowa da kowa.

“INEC ma ta tsara komai daidai. Amma jami’an da aka tura Jihar Kogi ne suka yi magudi. Sun bai wa Yahaya Bello takardar sakamako aka rubuta sakamakon tun kafin fara zaben,” in ji shi kamar yadda ya yi zargi.

Yayin da aka tattara sakamakon kananan hukumomi 18 daga cikin 21, INEC ta ce za a sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 59 na jihar a ranar Asabar mai zuwa.

INEC ta ayyana Ododo na APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 446,237, sai Ajaka na jam’iyyar SDP da kuri’u 259,052 a matsayin na biyu, yayin da Sanata Dino Melaye na Jam’iyyar PDP ya kare a matsayi na uku da kuri’u 46,362.