✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC ta sa ranar kammala zaben Kebbi da Adamawa

Akwai zabukan da INEC ta ayyana a matsayin wadanda ba su kammala ba saboda wasu matsaloli.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za ta kammala zabukan da ba a karasa ba a kasar.

Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin.

Baya ga wannan, a wani sako da hukumar ta kuma wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami’an hukumar a wannan Litinin din.

Hukumar ta ce sai a ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne za a karasa zabukan gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin da ba a karasa ba, sakamakon wasu matsaloli.

Ana iya tuna cewa, INEC dai ta ayyana zabukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.