Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta sanar da kammala shirye-shiryen zaben Kananan Hukumomin Abuja wanda za a gudanar a ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairun bana.
A ranar Alhamis ne Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu da manyan jami’an hukumar hadi da wakilan jam’iyyu suka shaida yadda aka rarraba muhimman kayayyakin aikin zaben a babban ofishin Hukumar da ke Abuja.
- NDLEA ta kama hodar Iblis ta N2bn a lokaci guda
- Coronavirus ta sake kama Yarima Charles na Birtaniya
A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar tun a ranar Talata, Farfese Yakubu ya bayyana cewa an tura Manyan Kwamishinonin Hukumar (National Commissioners) guda uku domin su sa ido kan zaben kananan hukumomin wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Mahmood ya ce za kuma a tura Kwamishimonin Zabe na jihohi (REC) guda shida su tallafa wa takwaransu mai kula da gundumar ta babban birnin kasar don ganin an yi zabe babu mishkila.
Yakubu, wanda ya ba da tabbacin cewa INEC ta sadaukatar da kanta wajen ganin an gudanar da amintaccen zabe, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaben da su mara wa hukumar baya ta hanyar ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ya yi la’akari da cewa idanun INEC na kan dukkan jami’an ta, “na wucin-gadi ne ko na dindindin,’’ domin a tabbatar da cewa sun bi doka da oda sosai.