✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta cire Alhassan Doguwa daga jerin zababbun ’yan majalisa

Duk da cewa an bayyana dan majalisar a matsayin wanda ya lashe zabe, babu sunansa a cikin jerin wadanda INEC za ta ba wa takardar…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, daga jerin wadanda suka lashe zaben da aka gudanar a makon jiya.

A yayin INEC ke shirin mika wa wadanda suka ci zaben kujerar sanata da na majalisar tarayya takardun shaida, Aminiya ta lura hukumar ba ta sanya sunan Alhassan Doguwa ba a matsayin zababben dan Majalisar Tarayya na mazabar Doguwa/Tudun Wada.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da cewa baturen zaben hukumar, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar cewa Alhassan Ado Doguwa na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’a 39,732, a yayin da babban abokin karawarsa, Yushau Salisu Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 34,798.

Amma a cikin jerin sunayen da INEC at fitar a ranar Litinin da dare na wadanda za a mika wa shaidar cin zabe, babu sunan Alhasannan Ado Doguwa.

Daga bisani hukumar ta bayyana cewa tursasa wa baturen zabenta aka yi ya sanar da sakamakon zaben da ke nuna dan majalisar ya lashe zaben ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Mun yi kokarin samun karin haske daga hukumar, amma hakan bai samu ba.

Mun kira Mataimakiyar Babban Jami’in Gudanarwa a Sashen Wayar da Kan Jama’a a Hedikwatar INEC da ke Abuja, Zainab Aminu Abubakar, ta waya, amma muka yi ta samun sabani. kuma har muka kammala hada wannan rahoton kuma tana kai wata wayar.

Dambarwar Alhassan Doguwa

Idan za a iya tunawa, bidiyo sanar da sakamakon zaben Doguwa da ya karade kafofin sada zumunta, ya nuna baturen zaben yana sanar da sakamakon a yayin da muryarsa ke rawa, lamarin da ya sa aka diga ayar tambaya.

Aminiya ta ba da rahoton yadda ’yan sanda suka tsare Alhassan Doguwa kan zarginsa da hannu a barkewar rikicin siyasa a mazabarsa, inda aka kashe mutane da dama da kuma kona sakatariyar NNPP a mazabarsa, zargin da ya musanta.

Rundunar ’Yan Sanan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar akalla mutum uku, a cibiyar tattara sakamakon zaben Doguwa/Tudun Wada, wanda daga bisani aka sanar cewa dan majalisar ya lashe.

Daba baya ’yan sanda suka tsare shi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin yin Umrah, suka kuma tsare shi.

Bayan nan ne aka gurfanar da shi a gaban wata kotun Majistare bisa zargin kisa, kona dukiya da kuma daukar makami ba bisa ka’ida ba.

Bayan an gurfanar da shi ne, kotun ta tura shi gidan yari, kafin daga bisani, bayan kusan mako guda ta bayar da belinsa a kan Naira miliyan 500.

Kotun ta kuma haramta masa shiga mazabarsa a lokacin zaben gwamnoni da ’yan Majlaisar jiha da ke tafe ranar 11 ga watan Maris da muke ciki.