Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana 11 ga watan Nuwamban 2023 a matsayin ranar gudanar da zabukan gwamna a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi.
Babban Kwamishina a hukumar, kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayanai da Ilimantarwa na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja, babban birnin kasar.
- Matasan da suka karkatar da kayan N25m sun shiga hannu
- An kone gidan gwamna a wani sabon rikici a Sudan
Ya ce INEC ta cimma wannan matsaya ne a taronta na mako-mako da ta gudanar ranar Talata.
Mista Okoye ya kara da cewa za a gudanar da zabukan fitar da gwani a jihohin uku daga ranar 27 ga watan Maris zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 2023.
A cewarsa, wannan mataki ne na cika sharuddan sashe na 28(1) na Dokar Zabe ta 2022 wadda ta wajabta wa hukumar ta fitar da sanarwar duk wani zabe kwanaki 360 kafin ranar da aka kayyade zaben.