✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ba za ta sauya jadawalin zaben 2019 ba – Farfesa Yakubu

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar zaben ba za ta canja jadawalin zaben badi ba da ta riga ta…

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar zaben ba za ta canja jadawalin zaben badi ba da ta riga ta futar bisa tanade-tanaden dokokin da ake da su.

 Farfesa Yakubu, wanda ya bayyana haka a Abuja a wajen taron ganawa da manema labarai a farkon wannan mako, bai cire ran za a iya duba jadawalin zaben ba, idan wani muhimmin lamari ya taso.

 “A ranar 9 ga Janairu, mun fitar da jadawalin yadda za a gudanr da zaben badi, bisa ikon da muke da shi, da kuma dokokin da suke akwai, kuma babu abin da ya canja. Akwai hujja ta zaben wadannan ranaku -kuma a daidai lokacin da dimokuradiyyarmu take dada karfi za mu gusa gaba daga rashin tabbas zuwa tabbas,” inji shi.

Ya ce, “A sanin hukumar babu wata doka da aka karya zuwa yanzu; kuma muna aiki ne a bisa dokokin da muke da su. Amma idan wani abu ya faru a gobe, za mu fito fili mu shaida wa ’yan Najeriya, amma ina jin ba muna aiki ne a bisa jita-jita ba.”

Shugaban na Hukumar INEC ya ce yana da tabbacin gudanar da zabe na gaskiya da adalci, bisa lura da yadda take ci gaba da tsoma muhimman masu ruwa-da-tsaki a harkokin zaben. 

Ya ce  hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye don tunkarar zaben na badi, kuma ya ce an dauki matakan da suka dace domin aiwatar da tanade-tanaden shiringudanar da zabe (EPP).

Shugaban ya ce hukumar tana kara kokari domin tabbatar da nakasassu sun samu sauki wajen jefa kuri’a ciki har da mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma tsofaffi.

Ya kawar da yiwuwar ba da dama ga kananan yaran da shekarunsu ba su kai ba, su jefa kuri’a a zaben na kasa da Hukumar INEC ke gudanarwa, inda ya nanata cewa hukumar zaben za ta yi “duk abin da ya wajaba wajen tsabtace aikin rajistar masu zabe ta yadda wadanda suka cancanta kawai ne za a bari su kada kuri’a.”