✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Indonesiya ta fara zawarcin Mourinho

Ministan matasa da wasanni na Indonesiya Imam Nahrawi ya bayyana cewa kasar ta fara zawarcin tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho don ya zama kocinta kuma…

Ministan matasa da wasanni na Indonesiya Imam Nahrawi ya bayyana cewa kasar ta fara zawarcin tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho don ya zama kocinta kuma tuni ta tuntubi kocin a kan wannan batu.
Jose Mourinho, wanda ya zama shahararre a fagen horarwa ya yi suna ne bayan ya samu nasarori a kulob din FC Porto na Fortugal da kulob din Chelsea na Ingila da na Inter Milan da ke Italiya da kuma na Real Madrid da ke Sifen.
Sai dai Ministan ya ce babbar matsala ita ce yadda za su iya biyan kocin albashin da ya nema na Fam miliyan 13 kwatankwacin Naira biliyan 6 a shekara.
Ministan ya ce da wuya Indonesiya ta iya biyan kocin wadannan kudade saboda matsalar tattalin arziki.  Amma Ministan ya ce duk da haka ya gabatar da bukatar daukar Jose Mourinho ga shugaban kasar Joko Widodo don ganin an shawo kan matsalar.
Indonesiya ta yanke shawarar nemo shahararren kocin da zai cigaba da horar da ’yan kwallonta ne wanda zai daukaka martabar kungiyar kwallon kafa ta kasar da ke neman yin fice a yankin Asiya da ma a duniya baki daya.