Gwamnatin kasar Indiya ta sanar da aniyarta ta kara mafi karancin shekarun aurar da mata daga 18 zuwa 21.
Rahotanni sun ce gwamnatin ta sanar da hakan ne yayin zaman Majalisar Kasar na ranar Laraba.
- Babu shugaban da zai iya kawar da ’yan bindiga a 2023 —Lai Mohammed
- An fara kaura a wasu kauyukan Zariya saboda matsalar tsaro
Yanzu haka dai a kasar, shekara 18 ce mafi karanci don aurar da mata, 21 kuma ga maza.
Hakan dai na nufin gwamnatin za ta sauya Dokar Haramta Aurar da Kananan Yara ta 2006, da kuma yin kwaskwarima ga Dokar Aure ta Musamman da kuma Dokar Aure ta addinin Hindu ta 1955.
A yayin jawabinsa na zagayowar ’yancin kan kasar na bana dai, Firaminista Narendra Modi ya bayyana bukatar yin hakan, inda ya ce, “Gwamnati ta damu matuka da lafiyar ’yan mata”.
“Domin kare ’ya’ya mata daga matsalar yunwa, ya zama wajibi a rika aurar da su a shekarun da suka dace,” inji Firaminista Modi.
Ko a farkon wannan shekarar, Jihar Haryana ta rubuta wa Modi wasika tana bukatar a kara shekarun aurar da mata daga 18 zuwa 21.
Jihar dai, wacce ke Arewacin kasar, ita ce ta fi karancin yawan mata in aka kwatanta da takwarorinsu maza a kasar ta Indiya.