Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya umurci dakarun kasar da su tunkari ’yan ta’adda su kuma shafe su daga doron kasa.
Shugaba Buhari ya ba da wannan umurni ne ranar Alhamis yayin bikin yaye hafsoshin soji 247 a garin Jaji da ke Jihar Kaduna da suka halarci kwas na 44.
- Ronaldo ya yi watsi da tayi mai tsoka na wata kungiya a Saudiyya
- An fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida
Ya ce shekaru 12 da suka wuce sun kasance cike da kalubale, ganin barazanar tsaro iri iri da suka addabi kasar.
A cewar shugaban kasar, matsalolin tsaron da suka addabi duniya iri daya ne, saboda sun kunshi kungiyoyi dabam dabam masu daukar makamai a yankuna daban-daban.
Shugaban Najeriyan ya ce kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan bindiga da dama su na cikin kasar, kuma abin da ya dace shine a tinkare su a shafe su daga doron kasa don kawo zaman lafiya.
Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bada gudummawar da ta dace don tabbatar da samun sakamakon da ake bukata.