Muhammad Ismai’il yaro ne da bai wuce shekaru goma sha ba amma ya yi fice akan kiwo da kuma sukuwa da doki. Ya ce yana iya sarrafa doki komin fadansa.
Wasu na tsoron doki, amma wannan yaron yana wuni ne a tsakan-kanin wadanan karfafan dabbobi, sannan kuma yana da burin ci gaba da karatu, ya zama dan sukuwar dawaki da kuma shaharren dan kwallon Polo.
Unguwan Doki na tsakanin makarantar Firamare ta Sultan Bello da Masallacin Sultan Bello a Unguwar Sarkin Musulmi Kaduna, akan titin Ali Akilu.
Wannan yankin gida ne ga matasa da ke koyon kiwon doki, da share masu muhalli da kuma yin kilisan manyan dawakan daga Unguwar Sarki zuwa Dandalin Murtala inda ake kilisa, sukuwa da yin wasan Polo.
Ana yi wa wasan Polo kirari da cewa “wasan sarakuna, kuma yana da hadari”. A wasu lokuta kuma wadannan yara masu kiwon doki ana hayarsu ne don su yi wasan sukuwa ko Daba a nan Kaduna yayin bikin aure ko lokacin da ake nada wa wani sarauta.
Abin mamaki shi ne yadda wani yaro ya yi fice a cikin masu hawan doki wanda yake da suna Muhammad Ismail, wanda aka fi sani da ‘Riba’.
Ya ce “Na fara koyon hawan doki ne kimanin Shekaru hudu da suka wuce, inda a yanzu na kware kuma fadan Doki ina iya hawan da sarrafa shi yadda nake so. Duk da shekaru na kadan ne, goma sha, kuma ina karatu a makarantar Firamare, amma ina iya hawa doki daya, in kuma ja linzamin wasu 3 zuwa filin motsa jiki daga Unguwan Doki zuwa Dandalin Murtala ko da siddi ko babu. Dalilin haka shi ne don a hora su kafin sukuwa ko wasan Polo ko sauransu.”
Ismail Riba ya ce ya taba samun hatsari yayin da ake sukuwar daba don taya wani daga cikin masu kiwon Doki da ya yi aure murna inda ya sukwano doki amma kafin ya ankara ya ci karo da wata mota da aka aje a gefen titi. Bayan ‘yan watanni yana jinya sannan ya warke ya ci gaba da harkar da yake so na sukuwa da doki, da karatu da burin zama shahararre da kuma zama ya sami Digiri.
Dokin da Ismail ya yi hatsari a kai sunansa “Sari”, kuma har yanzu shi ya fi son hawa. A dangane da tsawon lokacin da mutum zai dauka kafin ya kware a sukuwar Doki, sai Samaila ya ce, ya danganta da yadda mutum yake. Don dan koyo yana fara wa ne da tafiya, sannan sassarfa, sannan gudu.
Sai dai ya ce wadanda ke son koyon Doki suna iya bada na-goro a koya musu, musmmam wadanda ke zaunea Kaduna a dandalin Murtala.
Dangane da ko yana iya hawa Dokin Polo kakkarfa, kosashshe da aka kawo daga kasar Ajantina, sai Riba yace ko a yanzu aka sauke Doki daga jirgin sama daga kowace kasa zai iya hawansa komai girma do koshin sa.
Burin Riba shi ne “In karfina ya kai, zan so in koyin kwallon Polo don in kware sosai.”