✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina son na gaji kujerar Buhari a 2023 —Amaechi

A baya dai Amaechi ya sha musanta cewa yana son zama shugaban Najeriya.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a babban zabe na 2023 da ke tafe.

Amaechi ya bayyana aniyar tasa ce a wani taron siyasa da ya gudana ranar Asabar a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

“A yau na tsaya a gabanku domin na bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba,” in ji shi.

Tun bayan dawowa mulkin dimokuradiyya Amaechi ya shiga siyasa, inda ya rike kujerar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas daga shekerar 1999 zuwa 2007, sannan ya kuma zama gwamna a jihar daga shekerar 2007 zuwa 2015.

Ya kasance daya daga cikin mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake zabe a matsayin minista a wa’adin gwamnatinsa na biyu da ya faro a shekarar 2019.

Sai dai a baya Amaechi ya sha musanta cewa yana da wani buri na zama magajin Buhari.

Ko a wata tattaunawa da ya yi da Aminiya a shekarar da ta gabata ya ce babu wani shiri da yake yi wa zaben 2023, yana mai cewa “bacci zan yi na sarara.”

Sai dai a lokacin ya kara da cewa, yana da burin yin karatun digirin digirgir kasancewar ya riga ya yi digiri na biyu, “saboda haka idan na farka daga baccin nawa zan yi karatun digiri na uku don na koyar a jami’a.”

Ya zuwa yanzu dai Amaechi da tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu da gwamnan Kogi Yahaya Bello ne suka fito suka ayyana takararsu ta shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a kasar.