✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kawo min lissafin sabon albashi cikin awa 48 —Tinubu

Kungiyar kwadago ta ce ba za ta karbi karamin kari kan mafi karancin albashin N60,000 ba

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ministan kudi, Wale Edun, ya kai masa lissafin abin da za a rika kashewa wajen biyan albashin ma’aikata cikin kwana biyu.

Tinubu ya ba da umarnin ne a lokacin ganawarsa a Abuja da wakilan gwamnati a tattaunawar da ake da kungiyar kwadago kan karin mafi karancin albasi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin daKungiyar kwadago ta lashi takobin ba za ta amince da karin da bai ta kara ya karya kan Naira 60,000 da gwamnati take neman biya a matsayin mafi karancin albashi ba.

A ranar Litinin ne shugabannin kungiyar da wakilan gwamnati suka cimma daidaito da cewa gwamnati za ta kara mafi karancin albashin yahaura N60,000.

Bayan janye yajin aikin ne shugaban kungiyar ma’aikata ta TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa kungiyoyn ba kafewa suka yi a kan mafi karancin albashin Naira N494,000.

Osiffo ya bayyana wa wata da gidan talabijin na Channels cewa abin da suke bukata shi ne a ba wa ma’aikata albashi mai tsoka.

Game da ainihin abin da kungiyar za su amince daga gwamnati kuwa, Osifo ya ce wajibin ne kwamitin karin albashin ya nuna damwuwa game da halin da ma’aikata suke ciki a ba su albashin da ya dace da yanayin hauhawar fara shi da tattalin zargin da kasar ke ciki.

A cewarsa, wajibi ne albashin da ya dac da darar N30,000 a shekarar 2019 da kuma darajar N18,000 a shekarar 2014.

A ranar Litinin kungiyar kwadago ta fara yajin aiki saboda rashin amincewar gwamnati ta kara mafi karancin albashi daga Naira 60,000.

Daga bisani aka dakatar da yajin aikin bayan wakilan gwamnati sun yi alkawarin karawa daga N60,00 inda bangarorin za su ci gaba da tattaunawa na mako guda.

A kan haka ne kungiyoyin suka yi taro suka sansar da dakatadar da yajin aikin na tsawon mako guda. 

Da yake sanar da janye yajin aikin, shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero, ya kara da cewa sun ba wa gwamnatin damar bullo da mafi karancin albashi da ya dace, hadi da soke karin kudin wutar lantarki da kuma soke rabe masu amfani da wutar zuwa rukuni-rukuni. 

Tinubu ya umarci minista ya ba shi lissafin albashin ma’aikata cikin awa 48

A ranar Talatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ministan kudi Wale Edun, ya kai masa lissafin abin da za a rika kashewa wajen biyan albashin ma’aikata cikin kwana biyu.

Tinubu ya ba da umarnin ne a lokacin ganawarsa a Abuja da wakilan gwamnati a tattaunawar da ake da kungiyar kwadago.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce za a ci gaba da zaman da bangarorin, har da kamfanoni masu zaman kansu domin bullo da albashin da kowa zai yi na’am da shi.