✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina so in haura shekara 100 a Duniya —Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce ya burin ya kara shekara 20 a duniya kafin Allah Ya karbi rayuwarsa. Tsohon Shugaban Kasar mai shekara…

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce ya burin ya kara shekara 20 a duniya kafin Allah Ya karbi rayuwarsa.

Tsohon Shugaban Kasar mai shekara 83 a duniya ya ce yana kwadayin haura shekaru 100 yana raye.

Ya bayyana haka ne a Abeokuta a taron cikar babban basaraken lardin Gbagura, Oba Sabur Bakare, Jamolu na II shekara guda a kan karagar mulki.

Oba Sabur Bakare ya dare karagar mulki ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2019, ya kuma zama basarake na 9 a jerin wadanda suka rike sarautar Agura na lardin Gbagura a Jihar Ogun.

Obasanjo ya yi fatar samun halartar taron cikar basaraken shekaru 20 a karagar mulki; ya ce daga nan kuma ko ta Allah ta kasance, to Allah Ya Ya cika masa burinsa.

“Da ni za a yi bikin cikarka shekara 20 a karagar mulki, ko an gayyace ni ko ba a gayyace ni ba.

“Bayan an yi bikin cikarka shekara 20 a kan mulki da ni, idan Allah Ya so sai Ya karbi rayuwata, domin zuwa wannan lokacin na haura shekaru 100”, inji Obasanjo.

Cif Obasanjo ya bukaci basaraken da ya tabbatar da hadin kai a tsakanin sarakunan yankin da ma lardin al’ummar Yarbawa baki daya.

A karshe ya yi fatan wanzuwar zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin kabilar Ebga a Jihar Ogun.

 

 

%d bloggers like this: