✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina so in gaji mahaifina – Hanny Billy O.

Hanny Billy O, ya zama fitaccen suna a masana’antar wakokin zamani da aka fi sani da Hip-Hop. Yaro ne dan shekara goma da haihuwa, kuma…

Hanny Billy O, ya zama fitaccen suna a masana’antar wakokin zamani da aka fi sani da Hip-Hop. Yaro ne dan shekara goma da haihuwa, kuma da ne ga fitaccen mawain zamanin nan wato Bello Ibrahim, wand aka fi Sani da Billy O. A ttauanwarsa da Aminiya Hanny ya bayyana burin da yake da shi a harkar waka, ya kuma bayyana cewa yana hangen wakokin Hip-Hop za su danne kowace irin waka a fadin kasar nan.

 

Aminiya: Za mu so sanin tarihin rayuwarka?

Hanny: Suna na Hani Bello wanda aka fi sani da Hanny Billy O. An haife ni a watan Janairu na shekarar 2007.  A yanzu haka ina aji hudu na firamare a makarantar Ta’azimurrasul da ke Sharada cikin Jihar Kano.

Aminiya: Ya aka yi ka fara harkar waka?

Hanny: Zan iya cewa idan ana gadon waka, to ni gadarta na yi, domin na tashi na ga mahaifina a cikin harkar. Hakan ya sa na fara sha’awar yin waka. Sannan kuma na duba na gani a kasashen waje akwai kananan yara mawaka, amma mu anan ba mu da su, hakan ya kara min karfin gwiwa ni ma na fara waka. Da na fara sai ya zama mu biyu ne yara mawaka wato da marigayi Lil-Amir sai kuma ni.  Yanzu ga shi shi ya rasu saura ni kadai. Kodayake akwai yara da ake samu suna nuna sha’awar harkar, domin tun daga shigowarmu harkar, ni da marigayi Lil’amir sai yara suke

ta zuwa suna so su fara waka, a yanzu haka suna zuwa wajen mahaifina domin samun horo.

 

Aminiya: Shin kana rubuta wakar da kanka ne ko ya abin yake ne?

Hanny: Gaskiya ban taba rubutawa ba, sai dai idan mahaifina ya rubuta n ni kuma sai na rera. ko kuma uncle Mubarak M.K ma yana ba ni.

Aminiya: Zuwa yanzu wakoki nawa ka yi?

Hanny: A yanzu wakokina za su kai shida ko bakwai. Irin su Bye- Bye, sai Mun tara su  akwai kuma  Na tuba da akwai wace da mukai da uncle Mubarak wanda su suka fi yawa.

Aminiya: Ko ka taba yin waka tare da mahaifinka?

Hanny: Gaskiya ba mu taba yi da maifina ba, amma yanzu akwai wacce za mu yi kwanan nan domin har ma an rubuta ta.

Aminiya: Wane hange kake ga wakokin Hip-Hop a Najeriya, musamamn a Arewa?

Hanny: Gaskiya Hip-Hop yana kara samun daukaka a Najeriya Ina ganin nan gaba Hip-Hop zai danne duk wasu wakoki a Arewa saboda irin karbuwar da wakokin ke samu a wurin jama’a Da yawan mawaka suna yin waka mai kyau, sai dai duk da haka ana samun wasu kuma ba su yin mai kyau. Sai ka ji waka a maimakon a yi amfani da kalmomi masu kyau, sai ka ji an buge da yin amfani da kalmomin batsa. Gaskiya wanann ba abu ne mai kyau ba.

Aminiya: Ta yaya kake ganin za gyara harkar?

Hanny: Gaskiya ya kamata  mawaka su  tsaya su rika yin waka mai kyau cikin ilimi ba da jahilci ba,  a tsaya ayi gyara sosai. Kamata ya yi kungiya ta rika hukunta duk wanda aka samu da kalmomin batsa a wakarsa domin hakan na iya bata mana tarbiyyar al’ummarmu. domin mafi yawa wakokin namu na fadakarwa ne. Ya kamata mawaka su fahimci cewa ita daukaka Allah ne yake bayar da ita ba wai sai mawaki ya zo yana sa batsa a wakarsa zai smau daukaka ba. Abin da ake so a matsayinka na mawaki ka yi aikinka mai kyau tsakaninka da Allah.

Aminiya: Wane sako kake da shi ga masoyanka?

Hanny: Masoyana nagode sosai da irin soyayyar da suke nuna min. Ina gaida kowa da kowa. Ina yi musu albishir cewa su bude idanunsu da kunnuwansu kwanan nan zan yi bidiyon wata sabuwar wakata mai taken My Father and I wacce ake sa rai insha Allah za a dauki  bidiyonta a Legas karkashin kulawar mawaki B. Meri.

Aminiya: Baya ga waka me kake so ka zama idan ka gama makaranta?

Hanny: Gaskiya ina so in ga ina yin waka kamar yadda mahaifina yake yi. Sannan ina so bayan na kamala karatuna na zama matukin jirgin sama wato pilot ko kuma soja, wannan shi ne  burina a rayuwa.