✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙaurace wa shiga zanga-zanga —Zulum

Zanga-zanga ba za ta taɓa tabbatar da ɗorewar zaman lafiya ba.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ’yan Nijeriya baki ɗaya da su ƙauracewa shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa.

Zulum ya yi wannan roƙo ne a yau Laraba yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Borno da ke Maiduguri.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, a madadin wannan mataki da ’yan ƙasa ke shirin ɗauka, zai fi dacewa su shiga tattaunawa mai ma’ana domin zanga-zangar na iya haifar da tarzoma da tashin hankali a ƙasar.

Zulum ya tunatar da cewa har yanzu Jihar Borno ba ta iya farfaɗowa ba daga rikicin masu tayar da ƙayar baya da aka shafe tsawon shekaru 13 ana fuskanta wanda ya yi matuƙar mayar da hannun agogo baya a ci gaban jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa duk zanga-zanga ba ta kan turba ta daidai a matsayin wata hanya da za ta tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar ba.

Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin mahalarta taron sun haɗa da shuwagabannin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya, ƙungiyar lauyoyin Nijeriya.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da dakarun haɗin gwiwa, Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya CAN, Ƙungiyar Jama’atul Nasir Islam, ɗalibai, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata, ‘yan kasuwa, nakasassu, Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa da sauransu.