Kociyan Arsenal, Mikel Arteta, ya nemi afuwar magoya baya dangane da shan kayen da kungiyar ta yi har gida a hannun Brighton da kwallaye 3 da nema a ranar Lahadi.
Rashin nasarar da Arsenal ta yi ya sa kungiyar ta barar da damarta ta karshe a rige-rigen lashe kofin Firimiyar Ingila tsakaninta da Manchester City.
- Uwa ta rasu a wurin raba fada tsakanin ‘ya’yanta a Abuja
- Duk da rinjayen Erdogan akwai yiwuwar zuwa zagaye na biyu na zaben Turkiyya
Gunners dai ta shafe tsawon lokaci tana jagorancin teburin gasar ta Firimiya, a kokarin kawo karshen dakon shekaru 19 da ta yi a baya don kai kofin gida.
To sai dai Arsenal wadda ta lashe Kofin har sau 11 a tarihi, ta gamu da gagarumin matsin lamba a watannin baya-bayan nan daga City.
Wasanni 2 cikin 7 da Arsenal ta doka a baya-bayan nan kadai ta iya samun nasara, wanda ke nuna yiwuwar bankwananta da kofin na Firimiya daidai lokacin da ake da tazarar maki 4 tsakaninta da City, kuma tawagar ta Guardiola ke da wasa guda a hannu.
A jawabinsa gaban manema labarai Arteta ya ce salon wasan da Arsenal ta yi a zagaye na biyu na haduwar ta jiya sam ba abin karba ba ne.
A cewarsa a lissafe, iya lashe kofin na Firimiya ga Arsenal har yanzu abu ne mai yiwuwa amma a yanzu abin da ya fi muhimmanci garesu shi ne samar da gyara ga kura-kuren da suka yi a jiya.
Idan har Arsenal ta gaza nasara a haduwarta da Nottingham Forest a lahadi mai zuwa, kuma City ta yi nasara kan Chelsea a ranar 21 ga watan nan, kai tsaye tawagar ta Pep Guardiola ta lashe kofin karo na 5 cikin shekaru shida.