Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha a yau Laraba ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar AA.
Gwamnan ya samu rahotan sauya shekar ne a kafafan sadarwa na zamani cewa, wai Gwamnan ya koma AA.
Mai taimakawa Gwamnan akan watsa labarai Sam Onwuemeodo ne ya fitar da sanarwar inda ya ce, wannan abin mamaki ne Gwamnan ya fice daga Jam’iyyar APC duk da irin goyon bayan da yake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari.