✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina nan cikin koshin lafiya —Tinubu

A shirye nake na fara mulkin Najeriya daga ranar farko.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya musanta zargin da ake yi cewa ba shi da lafiya kuma watakila ya mutu.

Sai dai tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya bayyana cewa yana nan kalau kuma “ban janye daga takara ba.”

Wani bidiyo da dattijon mai shekara 70 ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna shi yana motsa jiki a kan keke, har ma yana cewa “a shirye nake na fara mulkin Najeriya daga ranar farko.”

“Wasu da yawa na cewa na mutu; wasu sun yi ikirarin na janye daga takara,” a cewarsa. “To…ba haka ba ne.”

Ya kara da cewa: “Ga gaskiyar lamarin: Garau nake, da lafiyata kuma a shirye nake na fara mulkin Najeriya daga ranar farko.”

Wannan ne karon farko da aka ji daga Tinubu tun bayan da ya fice daga Najeriya tsawon lokaci, inda abokin takararsa Kashim Shetttima ya dinga wakiltarsa a wurin taruka.

A ranar Laraba ne aka kaddamar da yakin neman zabe a hukumance yayin da Tinubu ke shirin fafatawa da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP da sauran ’yan takara 14 a zaben Shugaban Kasa na watan Fabarairu mai zuwa.