Wani mai gyaran janareto mai suna Junaidu Muhammad, ya ce duk da lalular rashin kafa da yake fama da ita, babu dalilin da zai sa shi ya yi bara, musamman ganin yadda sana’ar take rufa masa asiri. Matashin, wanda haifaffen garin Kafanchan ne da ke yankin karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna, ya rasa kafafunsa ne a lokacin da yake dan shekara tara, bayan ya yi fama da ciwon shan-inna.
A zantawarsa da Aminiya, a shagon da yake aiki a Rigasar Kaduna, ya ce albarkacin sana’arsa, yana samun abin da yake dogaro da kansa, yana tsira da mutuncinsa.
Ya ce: “Rikicin zaben shekarar 2011 ne ya tilasta min dawowa garin Kaduna. Da zuwana, sai na nufi wajen wani dan uwana mai suna Malam Salisu, inda na bayyana masa sha’awar da nake da ita kan koyon sana’ar hannu da kuma dogaro da kai. Wannan ya sa ya fara koya min gyaran janareto, wanda kuma har yanzu nake ci gaba da zama karkashinsa. Ina da kyakkyawar dangantaka da shi da sauran abokan aikina da kuma jama’a da suke zuwa wajenmu don bukatar aikinmu. A gaskiya ina samun karbuwa a wajen mutane, musamman wadanda na taba yi wa aiki, wadanda sukan yaba sosai da aikin nawa.”
Junaidu ya ce a halin da ake ciki shekararsa 24 kuma kafin zuwansa Kaduna, ya yi sana’ar sayar da katin waya da kuma gyaran rediyo.
Ya bayyana wa wakilinmu cewa ya yi makarantar firamare da sakandare, lamarin da inji shi, ya sa ba shi da wani babban buri a halin da yake ciki da ya wuce komawa makaranta domin ci gaba da karatunsa.
Ya ce a sanadiyyar sana’arsa ya hadu da manyan mutane da dama. “Akwai wani bawan Allah, wanda ta sanadiyyarsa ne na samu gurbin zuwa makarantar kwamfuta, inda na samu takardar shaidar Difloma, amma babu wani taimako daga gwamnati da na taba samu zuwa yanzu.” Inji shi.
Ina gyaran janareto ne domin kare mutuncina – Janaidu Gurgu
Wani mai gyaran janareto mai suna Junaidu Muhammad, ya ce duk da lalular rashin kafa da yake fama da ita, babu dalilin da zai sa…