Edita ka ba ni fili in yi tsokaci kan batun tallafin da aka ce an tara don ba wadanda iska ta yi wa barna a daminar bana a garin Bauchi. Hakika murnar da wadanda barnar iska ta shafa ta koma ciki sakamakon yadda aka gaza rarraba tallafin gare su har zuwa yanzu. Shin wadanda suke kula da tallafin suna murna ne da aukuwar bala’in ko kuwa tsabagen rashin imani da tausayi ne ya jawo suka danne tallafin ruwa yana ci gaba da lalata gidaje da gine-ginen jama’a ba tare da an mika musu tallafin sun gyara ba. Abin takaici hatta ma’aikatu da ofisoshin gwamnati kashi 80 cikin 100 suna nan gwamnati ba ta gyara ba.
Don haka ina kira a hanzarta mika tallafin ga wadanda iskar ta yi wa barna cikin gaggawa don kada sauran gine-ginensu su karasa rushewa.
A karshe ina kira ga fadar Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu, ta fito ta yi bayani kan tallafin da aka mika ta hannun Sarkin domin wanke shi da masarautarsa, saboda mutane sun fara guna-guni suna ganin kamar kudin suna hannun masarautar ce ta yi shiru.
Alhaji Gambo Abdullahi Bababa, Shugaban Kungiyar Masu Harhada Magungunan Gargajiya ta Jihar Bauchi. 08023622651 da 07032096837
Kira ga ’yan kasuwa
S |
alam Editan da fatan kana lafiya, ina kira ga ’yan kasuwa masu karamin karfi kada su sayo kaya bashi su sayar bashi domin yin hakan zai iya jawowa bashin ya hau kanku domin in kuka bayar da bashi ba kowa ne zai biya ba kun ga a nan bashi ya dawo kanku ke nan da fatan kun ji wannan kira nawa.
Daga Malam Malam Mai Zanen Hula Gololo, 08032822433
Kira ga Salihu Maidaji
Assalamu alaikum Edita. Ina son ka isar min da sakona ga dan majalisa mai wakiltar Gada ta Gabas a Jihar Sakkwato, Alhaji Salihu Maidaji. Mu mutanen Gabas Gada ba mu yarda da wakilcinsa ba, saboda bai cika mana alkawarin da ya yi mana ba. Don haka mu mutanen Duka-Maje ba mu so.
Daga Bashar Garba Duka-Maje, 08167791483
Jinjina ga Shugaba Buhari
Salam Edita, ka ba ni dama in jijina wa Shugaban Kasarmu, kan namijin aikin da ya dauka yana yi a kasar nan, masamman a Arewa maso Gabas. Allah Ya kara masa lafiya kuma ina yi wa Shugaban Hukumar DSS da aka nada kwanan nan da ya ba marada kunya ya rike amana bisa ga aikinsa muna yi masa addu’a. Allah Ya taimake shi riko.
Daga Jibrin Dangombe, 09037253237.
Karshen bashi bauta
Salam Aminiya. Karshen bashi bauta, idan har ka kasa biya. Ga wahalhalun sharuddodi kafin a ba ka da wannan mai zai hana mu je mu sayo fasaha daga kasashen da suka ci gaba a duniya tunda muna da zakakuran matasa su fitar da hanyoyin da za su kai mu ga gaci, maimakon wannan bashi da muke ciyowa tun sama da shekara 60, har yau sai ci gaban mai hakar rijiya muke. Mu dubi yadda yanzu kasar Moroko ke haskawa a cikin kasashen Afirka a inda ta rungumi tata fasahar ta yi watsi da harkokin Turawan Yamma kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Daga Basiru Dan Bazazzagi 08058591624.
Talauci ya yi wa ’yan Najeriya yawa
Assalamu alaikum jaridar Aminiya mai albarka. Ina kira ga Shugaba Buhari cewa talauci ya yi wa kasar nan yawa. Kuma ya kamata a kara wa Naira karfi.
Daga Ali Badina, Shugaban Matasan Jihar Legas 09069158247.
Godiya ga Gwamna Tambuwal
Assalam Edita, mu Sakwkwatawa ba abin da za mu ce a kan Tambuwal sai fatan alheri domin rabanmu da samun gwamnati mai kaunar Sakkwatawa kamar tasa tun lokacin tsohon Gwamna Bafarawa. Mun gamsu kuma mun yaba, fatanmu Allah Ya yi masa jagora da shi da jagoran matasan Sakkwato Alhaji Mu’azu Zabira Allah Ya yi musu jagora amin.
Daga Musty Sakkwato 08034068363.
Akwai gyara ga ’yan Majalisar Dokoki
Kaico! Naka shi ke bayar da kai. A zaben shekarar 2015 da ya gabata jama’ar kananan hukumomin Katsina mun saki reshe muka kama ganye, inda muka kyale jinin sarauta muka zabi talaka a matsayin wakilinmu a Majalisar Wakilai. Mun kuma yi haka ne lura da ganin talakan kamar shi ne wanda ya san irin halin da muke ciki na kuncin rayuwa. Sai ga shi zaben ya zama na tumun-dare. Domin wakilin namu tunda muka tura shi zuwa Abuja shi ke nan sai ya yi watsi da wadanda suka zabe shi, ba zuwa ba aiki ballan tana yin aikin da zai inganta rayuwar jama’a.To amma za mu yi masa baki a 2019 inda mu ma za mu yi watsi da shi.
Daga Haruna Muhammad Katsina. 07039205659.
Allah Ya kawo saukin kwalara
Fatan alheri Aminiya. Al’ummar Jihar Borno muna taya ku addu’ar Allah Ya kawo muku saukin wannan cuta ta kwalara da ke lakume rayukan al’umma da ma duniya baki daya.
Daga Alhaji Umar Foreber Gashuwa 0810800
Martani ga Gwamnan Ribas
Assalamu alaikum Edita, fatan alheri a gare ka. Ka ba ni dama domin in mai da wa Gwamnan Jihar Ribas Nyensom Wike martani a kan kiran da ya yi ga ’yan Najeriya da kuma sukar Jam’iyyar APC. A gaskiya mu ’yan Najeriya muna tare da Jam’iyyar APC ganin yadda take kokarin kawo wa kasa ci gaba kuma a 2019 APC za mu yi sak.
Daga Garba Sabiyola Gashuwa Jihar Yobe 08096284154.
Zaben Osun darasi ne ga Jam’iyyar APC!
Fatan alheri Edita. Domin Allah ku ba ni dama in yi hannunka mai sanda ga mahukuntan Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, kan koma-bayan da ta fuskanta a Jihar Osun. Saboda haka ya kamata shugabannin jam’iyyar ta APC su farka daga dogon barcin da suke yi, domin magance rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar a wasu jihohin kasar nan tun kafin dama ta kubuce musu. Na gode jaridarmu amintatta.
Daga Idriss M Idriss Damaturu Jihar Yobe 08033775767
Zuwa ga Bishop Stephen Oni kan takarar Buhari
Da fatan Editan Aminiya za ka taimaka min da fili in bayyana ra’ayina dangane da limamin Anglican Bishop Stephen Oni wanda ya ce a zaben 2019 Shugaba Muhammadu Buhari kada ya sake tsayawa takara, a bar wa matasa. To mu matasa muna goyon bayan Muhammadu Buhari don ya yi abin da shugabanni da suka wuce ba su yi ba. Z a mu zabe shi a 2019 ya yi mulki zuwa 2023 daga nan a samu matasa.
Daga Mohammed Babayo, Keffi Jihar Nasarawa 08096954874
Gaisuwa ga Kwankwaso
Salam Edita, ka ba ni dama in gaishe da maigida Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Allah Ya taimaki mai nufin Najeriya da mutanen Najeriya da alheri. Allah Kai kadai ne masanin abin da ba mu sani ba, ya Allah muna tuba a gare Ka, Ka gafartamana laifukanmu ka ba mu shugaban nagari.
Daga Suraj Dan Murja, Tashar Mota Jabi, Abuja 07013732429.
APC da PDP duk daya ne
Assalamu alaikum Edita. Ina mika gaisuwa mai yawa zuwa gare ku, a matsayina na dalibi, na tsaya na yi bincike sosai, na gano cewa duk jam’iyoyin nan APC da PDP da sauransu duka daya ne. Bambanci shi ne daga wanda yake mulkinku in ya yi adalci sai a jingina ga jam’iyyar, in kuma ya yi batanci sai a jingina ga jam’iyyar. Ka ga kana da damar komawa duk inda kake so, ka ga alamun adalci akwai Allah. Allah Ya ba mu shugaba adali a cikin kowace jam’iyya, amin.
Daga Yahaya Tsamaye Gobir 08100181548.
Sakon ta’aziyya
Assalam. Muna mika ta’aziyyarmu ga al’umma musamman malamai da daliban Hausa a fadin duniya bisa ga rasuwar babban malami a fannin nazarin harshen Hausa na Jami’ar Bayero, Dokta Habibu Sani Babura. Allah Ya jikansa, mu kuma Ya kyautata karshenmu, Amin.
Daga Isa Usman Tumu, Karamar Hukumar Akko. 07060563008.
Gaisuwa ga masoyan Buhari
Salam Edita, ina son in mika gaisuwata ga ’yan Najeriya masoya mulkin gaskiya na Baba Buhari. Allah Ya maimaita daga masoyin Buhari da ’yan uwa ’yan Najeriya sai Baba 2019.
Daga Alhaji Mudassir M. Madawaki, Bakori Jihar Katsina 07063102009.
A hana tsofaffin gwamnoni zama sanatoci
Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni dama in yi kira da babbar murya ga tsofaffin gwamnonin Najeriya cewa ya kamata ku daina fitowa takarar sanata bai dace ba wallahi ka yi Gwamna shekara takwas, kuma saboda mutuwar zuciya ka nemi takarar Sanata. Akwai wani tsohon Gwamna shekararsa 12 a majalisar babu abin da ya tsinana gara ma kansila da irinsu ya kamata Gwamnatin Tarayya ta sa doka a kan tsofaffin gwamnoni su daina tsayawa takarar Sanata a kasarnan.
Daga Abdullah M. Inuwa, Kabo Jihar Kano. 08067880649
Kira ga Majalisar Dokokin Najeriya
Salam fatan, alheri ga jaridar Aminiya da kuma dukan ma’aikatan wannan jarida mai albarka. Shawarata ga Majalisar Dokokin Najeriya su mai da wa’adin mulkin Shugaban Kasa da gwamnoni ya zama shekara takwas lokaci guda maimakon hudu sau biyu, saboda maganin rigima. Muna rokon Allah ya zaunar da mu lafiya, Amin.
Daga Abubukar S. Yakubu, Abuja 08024929140.