✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina Firmino zai koma bayan raba gari da Liverpool?

Firmino ya rika fuskantar matsalar zaman benci karkashin jagorancin Jurgen Klopp.

A karshen wannan kaka ne dai Roberto Firmino zai raba gari da Liverpool sakamakon karewar da kwantiraginsa zai yi a watan Yuni kuma ba tare da sabuntawa ba, daga kungiyar wadda ke ganin mugun koma baya a wannan kaka.

Dan wasan gaba na Brazil ya zura kwallo a wasansa na karshe da ya doka wa kungiyar ranar Lahadi wanda ta yi canjaras kwallaye 4 da 4 tsakaninta da Southampton wadda ta kammala gasar a matsayin ta karshe a teburi.

Akwai dai jita-jitar da ke alakanta Firmino da komawa Barcelona kamar yadda Daily Mail da Marca a Spain suka bayyana cewa tuni kungiyar ta Catalonia ta sanya dan wasan na Brazil a sahun cefanen da ke son yi karshen kaka.

Firmino wanda ya shafe shekaru 8 a Liverpool tun gabanin karewar kwantiraginsa, ya rika fuskantar matsalar zaman benci karkashin jagorancin Jurgen Klopp, inda ma har wasu jita-jita a baya suka bayyana yiwuwar sayar da shi gabanin karewar kwantiragin nasa.

A bangare guda, ita ma kungiyar ta Barcelona duk da nasararta ta lashe kofin gasar La Liga har yanzu ta na bukatar samar da wasu gyare-gyare don cike gibin da ta ke da shi wanda ya hadddasa mata mummunar ficewa daga gasar zakarun Turai a kakar da muka yi bankwana da ita.