Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce yana fata man fetur din Najeriya ya kare, inda ya ce kudin da ake samu daga man fetur ne babban abin da ke kawo tarnaki ga tunaninmu na kirkiro abubuwa.
Gano man fetur a Najeriya ne ya jawo kauracewar kwararru zuwa kasashen waje, inda ya ce zai fi kyau man ya kare don mayar da kasar kan hanya ta kwarai.
Gwamna El-Rufa’i, ya bayyana haka a ranar Asabar da ta gabata a Ibadan, wajen bikin ‘Ganawa da Jama’a da Ranar Ma’assasa’ wadda Cibiyar Bunkasa Tsare-Tsare (DPC) ta shirya domin tunawa da fitaccen masanin tattalin arzikin nan, Farfesa Ojetunji Aboyade ta bana.
Ya ce “Saboda Najeriya tana samun “kudi a bagas” daga man fetur, sai kasar ta yin asarar tunanin kirkiro abubuwa kan yadda za a bunkasa sauran hanyoyin samun kudaden shiga tare da fadada hanyoyin tattalin arziki.”
Ya kara da cewa: “Yayin da muke fama da masanan da suke gudu daga kasar nan, yaya za a yi mu jawo ’ya’yanmu da suke kasashen waje da kwararru irinsu kamar yadda kasashen China da Indiya suke gani a yanzu? Wadannan ne kalubake ne da suka shafi tunaninmu kan kudin bagas na man fetur. Man fetur din yana karewa zai fi zama alheri ga sake tunanin kasar nan, mu kasance masu kirkiro abubuwa da girmama kwarewa da nasarar da aka samu a fannin ilimi. Muna samun kudi a bagas, ba mu karbar haraji, harajinmu kashi shida ne kacal na kudin shigar kasar nan; wannan yana nufin kashi 21 cikin 100 na jimillar adadin. Mun daina girmama fasaha da kwarewar da muke da su a jami’o’inmu saboda muna samun kudin banza.”
“Wannan babban abin bakin ciki ne, zan so man fetur din ya kare ta yadda za mu fara amgani da tunaninmu, domin mun daina amfani da tunaninmu, mun daina girmama ilimi saboda samun kudi a bagas,” inji El-Rufa’i.
Gwamna El-Rufa’i ya ce Najeriya ba ta da tsarin ci gaba mai dorewa da zai taimaka mata wajen ci gaba, inda ya ce, “Abin takaici ne cewa Najeriya ba ta da isassun ’yan sanda, ana bukatar karin jami’ai da hanyoyin samun bayanan sirri da horo mai inganci da kayayyakin kimiyya domin amfanin hukumomin tsaro, kafin kasar ta samu ingantaccen tabbaci ga tsaronta. Kuma koda akwai wadannan abubuwa, ana muhawara kan ko tattara aikin dan sanda a wuri daya da fasali da yawan ’yan sandan da suke kula da kimanin mutum miliyan 200 za su wadaci jama’a masu kabilu da harsuna da al’adu mabambanta a kasa irin Najeriya,” inji shi.