Yanzu dai ta tabbata cewa kisan miji ko yanke al’aurarsa da wasu mata ke yi da sunan soyayya ko kishi ya fara zama ruwan dare game duniya. Idan kuwa haka ne, to mene ne abin yi? Zama za mu yi a yi ta kashe mu daya bayan daya, ko tattauna zancen za mu rika yi a shafukan yanar gizo da sauran dandali kawai?
Tun da dai galibinmu maza muna sha’awar zama da mace fiye da guda, to kuwa lallai akwai matakan da ya kamata mu dauka, domin yi wa tufkar hanci.
Da farko dai jahilci ne mace ta dauka halittarta da ta namiji duka daya ne. Ma’ana, kowa ya tsaya a kan abokin zamansa. Kuma ko da namiji ya ce maki ba zai sake yin aure ba, karya yake maki. Tun farko ma kada ki yarda, domin haka Allah Ya halicce shi kuma Shi Ubangiji da Ya halicci maza da mata, Ya ce mazan su auri mace fiye da guda. Sannan su maza su daina yaudarar mata suna ce ma su ba za su sake auren wata mace ba, kodayake akwai wadanda za su iya wadatuwa da mace guda din amma ba su da yawa a cikin al’umma. Wannan ita ce gaskiyar magana.
Haka kuma ya kamata mata su ji tsoran Allah su rika barin maza suna karin aure, idan ma har ba za su karfafa masu gwiwar yin karin ba; domin duk sa’adda mace ta kafe ta hana mijinta kula wata ko auro wata, to kar ma ta yaudari kanta, domin idan ba mai tsaron Allah ba ne, zina zai rika yi a waje, karshe ma ya shigo mata da wani ciwo cikin gida. Idan kuma yana da imani, to dole sai ya auro wata. Kai ko ma bai auro watan ba, dole dai sai ya yi sha’awar wata bayan ke. Domin gwargwadon imanin mutum ma gwargwadon sha’awarsa, domin fitina ce, Allah kuma Bai son ka fitinu din. Don haka yawancin Annabawa suke auren mata da yawa. Misali, Annabi Dawud (as) ya auri mata 100, Annabi Suleiman (as) ya auri mata 1000, amma babu wacce ta yi kisan kai cikinsu.
E, lallai ne dole mace ta yi kishi, to amma ba na hauka ba. Ni dai a ganina babu yadda za a yi mace ta kashe mijinta saboda tsabar sonsa kamar yadda wasu matan suke gani. To, wace irin soyayya ce wannan? Sannan maza ma suna da wani sakaci, da zarar mutum ya hau dokin soyayya sai ya rika sakin alkawura kamar sakarai, sannan daga baya su dame shi. Haka kuma wasu mata da yawa musamman ’yan boko na kallon mazansu na aure a matsayin abokan zama kawai, babu wanda ya fi wani a cikinsu. Ba lallai ne idan ya ba da umarni a bi shi ba. Wannan kuma babbar halaka ce.
Don haka muddin muna son mu zauna lafiya a duniya sannan mu sadu da Ubangiji lami lafiya, to mu koma ga littafinSa saboda akwai karancin martaba dokokin addinin ga wasunmu. Wata yarinyar ma idan aka karanta mata wata ka’ida har sabo da ashar take yi, wai babu ruwanta da Alkur’ani saboda irin rayuwa da tarbiyyar da iyayenta suka ba ta. Dole mu kalli wadannan abubuwa kamar haka:
1-Me addini ya ce a kan auren mace fiye da guda? 2-Wace rawa iyaye ke takawa game da tarbiyya? 3-A kan wane mizani muke gina auratayyarmu a yau? 3-Wace mace ko namiji ya kamata a aura? 4-Me ya kamata hukumominmu su yi?