✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da yakinin Najeriya za ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya -Jose Mourinho

Shahararren kocin kulob din Chelsea na Ingila kuma haifaffen kasar Potugal Jose Mourinho ya bayyana cewa yana da tabbacin Najeriya za ta tabuka abin-a-zo-a-gani a…

Shahararren kocin kulob din Chelsea na Ingila kuma haifaffen kasar Potugal Jose Mourinho ya bayyana cewa yana da tabbacin Najeriya za ta tabuka abin-a-zo-a-gani a gasar cin kofin duniya da za a fara a mako mai zuwa.
Hasalima kocin ya ce Najetriya ce za ta zama ta biyu a rukunin F inda za ta fafata da kasashen Iran da Ajantina da kuma Bosniya Hergobina.
A tattaunawar da kocin ya yi da kafar wasanni ta Yahoo Sports ya lissafa kasashe 16 da yake da yake ganin za su haye mataki na biyu a gasar.
Ya ce saboda yadda suke huldar arziki da kocin Holand Luis ban Gaal ya tabbatar kasar ce za ta gama a matsayi na biyu a rukunin B baya ga kasar Sifen.&nbsp “A gaskiya ina da son kai don haka na zabi Holan ta kasance ta biyu a rukunin B saboda abokina ban Gaal”.
Haka kuma ya ce a rukunin C ya zabi kasar Kwaddebuwa da kuma Greece ne su haye zagaye na biyu maimakon kasashen Kolombiya da Japan.
A rukunin D kuwa kocin ya ce bai tantance kasashe biyu da yake jin za su kai zagaye na biyu a gasar ba saboda duk kasashen da za su fafata a rukunin karfinsu ya kusa ya zo daya.&nbsp &nbsp kasashen da za su yi wasa a rukunin sun hada da Ingila da Italiya da Uruguay.&nbsp Ya ce “dole ne in yi taka tsantsan domin idan na ce Ingila ba za ta kai labari a rukunin ba maiyiwuwa su kore ni daga harkar horarwa a kasarsu musamman ganin cewa yanzu haka a can nake aikin horar da kulob din Chelsea”.
Sai rukunin F inda ya zabi Najeriya ta zama ta biyu baya ga Ajantina saboda dan kwallonsa John Obi Mikel da ya kasance a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya.