Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa yana da koshin lafiyar da zai iya shugabancin kasar nan.
Dan takarar ya bayyana haka ne a wani taron da ya yi da jiga-jigan jam’iyyar APC da kuma manyan ‘yan kasuwar Jihar Kano a ranar Asabar.
- HOTUNA: Bikin kaddamar da yakin neman zaben Tinubu a Kano
- Ambaliyar Ruwa: Tinubu ya ba Kanawa tallafin Naira miliyan 100
Tinubu ya musanta ikirarin da ake yi na cewa, ba shi da koshin lafiyar da zai iya mulkin kasar nan.
“Ba takarar tseren fanfalaki na ke yi ba, ko kuma takarar gasar kokawa na cin kambin duniya.
“Wadanda ke cewa ba ni da koshin lafiya, su kalle ni da kyau na yi kama da mara lafiya?” in ji Tinubu.
Dan takarar Shugaban Kasar ya yi wa kungiyar ‘yan kasuwar alkawarin idan an zabe shi, zai ba marada kunya, ta hanyar sauke duk alkawuran da ya dauka.
Aminiya ta ruwaito cewa, Tinubu ya sauka Jihar Kano tare da jiga-jigan jam’iyyar APC na Kasa da na jiha, da kuma gwamnonin jam’iyyar, inda ya kaddamar da yakin neman zabensa.
Kazalika, ya kaddamar da wasu ofisoshin yakin neman zabe, da kuma ganawa da wasu manyan masu fada-a-ji a jihar.