Lura da yadda yaudara ta zama ruwan dare a cikin al’umma, inda mata ke dora alhakin ga maza, su kuma maza su dora wa mata laifin, koma yaya ne; da ni da ku mun yi ammana cewa yaudarar nan tana taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar alaka a tsakanin matasanmu maza da mata, kuma tana kawo babban tarnaki ga auratayya a cikin al’umma.
A duk lokacin da namiji ya yaudari mace ko wata ta yaudari namiji daga lokacin sukan tsani auren, mace kan tsani duk wani namiji, haka shi ma namiji kan tsani duk wata mace. Sukan ji duk wata sha’awar aure ta fita daga gare su.
Wannan ne ya sa na dauki bangaren maza don fitowa da ’yan mata irin hikimomi da dabarun da maza ke bi wajen yaudararsu ta hanyar kalamansu, domin duk yadda namiji ya kai wajen yaudara, to duk lokacin da ya kwankwasa ki ya ji babu wata kofa da zai yaudare ki to zai hakura. Ke dai ki nazarci wadannan muhimman bayanai kamar haka:
1. Ko kin san jikinki tamkar sabon zinari ne a cikin leda sai namijin da ya biya sadakinki ne zai iya ganinsa? Ki yi kokarin kare mutuncinki.
2. Ko kin san duk saurayin da yake gudun haduwa da iyayenki ko magabatanki, mayaudari ne ba mai son yin aure ba?
3. Ko kin san duk saurayin da ya fiye magana a kan kirar jikinki da kyan fuskarki, mai sha’awa ce ba mai SO ba?
4. Ko kin san duk saurayin da ya cika tattara hankalinsa a kan ado da kwalliyarsa, ba zai iya kula da gida ba?
5. Ko kin san duk saurayin da yake damuwa da zancen dukiyar gidanku ba halayenki ba, ba son aure yake yi miki ba?
6. Ko kin san duk saurayin da ya fi damuwa ya taba miki hannu ko jiki, ba son aure yake yi miki ba?
7. Ko kin san duk saurayin da yake son ki rika zuwa wurinsa (dakinsa), ko ki rika raka shi wurare, ba son Allah da Annabi yake miki ba?
8. Ko kin san duk saurayin da ya cika labarin matsayi da darajarsa, ba zai iya mutunta ki ba?
Wadannan da wasunsu na daga cikin dabi’un samarin da ya kamata ’yan mata da zawarawa su lura da su don gudun fadawa tarkon mayaudarabn samarin zamani.
Saura me? Lallai kwadayinki da son abin duniyarki na taka rawa wajen yi miki yaudara, matukar kina da kwadayi a nan matsalar take; masu iya magana na cewa; idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira.
Ibrahim Hamisu, ya rubuto ne daga Kano.
Za a iya samunsa ta: O8060651676.
Imel: [email protected]