Shaye-shaye dai na nufin amfani da wani abu da zai gusar wa mutum da hankali ko ya saka maye ta hanyar sha ko shinshinawa ko ci ko busawa ko kuma allura.
A zamanin baya, sai dai mu ji labarin irin wannan dabi’ar a kasashen ketare, wasa-wasa har ta shigo cikin kasarmu da al’ummarmu.
- Yadda Dalibi ke kokarin mayar da gashin kaji ya zama abinci
- PDP ta kalubalanci Buhari a kan karin kudin wuta
Babban abin takaici halayya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ta zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa.
Da yawa mutane ba su san me ke kawo wannan dabi’ar ta shaye-shaye ba, ko kuma suna kan hanyar fadawa shaye-shayen ba tare da sun sani ba.
Kadan daga cikin abin da ke kawo shaye-shaye sun hada da:-
- Shan magani ba da izinin likita ba: Da yawa muna da wannan dabi’ar, da mun ji rashin lafiya sai mu je Kemis mu sayo magani mu fara sha ba tare da likita ya gwada mu ba ya tabbatar mana da abin da za mu sha din ko ya dace da jininmu.
- Rashin amfani da magani a kan ka’idar da aka dora mu: Misali an ce ka yi mako daya kana sha, sai ka yi kwana uku ko kuma ka zarce adadin kwanakin, ko kuma an ce kasha cokali daya sai ka sha rabin kwalba.
- Matsalar bai wa yara rashin kulawa: Wasu iyayen basu damu da jan ’ya’yansu a jiki ba, har su san damuwarsu, irin wannan yana kawo matsalar da a Turanci ake Kira ‘Depression’. Kuma ana iya samun wannan matsalar a tsakanin ma’aurata da suke samun matsala, daga haka shaye-shaye za su iya biyo baya.
- Mu’amala da abokai masu shaye-shaye: Wannam ma yana janyo matsalar a al’umma.
- Wasu iyaye mata suna da sakacin shan magani barkatai idan suna da ciki, wanda hakan na iya taba jinjiri kafin ma ya zo duniyar an koyar da shi. Ko kuma mata masu ajiye magani barkatai a ko ina suka ga dama, har yaro ya dauka ya sha.
- Wani lokaci likitoci kansu suna janyo wannan matsalar ta hanyar hada mutum da abin da jininsa ba zai iya dauka ba.
Wadannan su ne hanyoyi sanannu da ke iya haddasa matsalar shaye-shaye a cikin al’umma.
Illar da shaye-shaye ga al’umma Idan mutum ya riski kansa a yanayin shaye-shaye, hakika rayuwarsa tana canjawa gaba daya.
Abin zai taba lafiyarsa da mu’amalarsa da mutane. Aikin sa kai har hankalinsa zai iya rasawa baki daya ko a wayi gari mutum ya rasa ransa, to mene ne ribar hakan?
A cikin al’umma duk wata barna, ta’adanci da rashin sa ido za ka ga sun faru sai ka tarar da mai aikata wannan abin yana da dabi’ar shaye- shaye. Misali ’yan fashi masu yi wa mata fyade da barayi.
Shaye-shaye na kawo mutuwar aure da rasa aikin yi da talauci da rashin zama lafiya da mutane da tabarbarewar tarbiyar yara da fadace-fadace.
Ashe wannan zai nuna mana cewar matsalar shaye- shaye ba karamar matsala ba ce ga rayuwar mutum da al’umma baki daya.
Abin tambaya yanzu yaya za a yi a magance wannan matsalar ta shaye shaye?
Yadda za a magance shaye-shaye
Kamar yadda bayani yazo a baya a kan abin da ke kawo shaye-shaye da kuma illolinsa ga mutum da al’umma baki daya.
Yanzu kuma zan yi bayani a kan hanyar kare kai daga fara shaye- shaye da kuma hanyar kawar da shi baki daya.
Yawancin mutane suna fara shaye- shaye saboda wata damuwa ko kaddara da ta hau kansu suka kasa jurewa, ko kuma zama da masu irin wannan dabi’ar.
Wadannan hanyoyin za su taimaka wurin hana faruwar matsalar shaye-shaye:
- Yana da kyau mutum ya fuskanci matsalarsa ya yi kokarin magance ta maimakon ya fada shaye shaye.
- Iyaye yana da kyau su dinga jan yaransu a jiki domin su san damuwarsu, kuma su san irin abokanan da suke mu’amala da su.
- Maza ya kamata su daina tsangwamar matansu, su dinga jan su a jiki, da kuma sanin irin kawayen da suke hulda da su.
- Hakazalika, maza su nisanci mu’amala da masu irin wannan dabi’ar kuma su kasance masu karbar kaddara a duk yadda ta zo musu, ka da hakan ya zama dalilin fara shaye-shayensu.
- Mu guji shan magani ba tare da izinin likita ba, kuma mu kiyaye ka’idojin shan maganin.
- Mata su guji amfani da magani barkatai a lokacin da suke da juna biyu ko kuma ajiye magani barkatai saboda ka da yara su dinga dauka suna sha.
- Likitoci su san aikinsu da kyau, su kiyayi bai wa mutum maganin da ya fi karfin jininsa ko zai iya janyo masa matsala.
Hanyoyin da ya kamata kuma abi domin kawar da matsalar shaye- shaye sun hada da:
- Janyo masu matsalar a jiki, ana nusar da su illar hakan, a guji tsangwamar su da kyara.
- Ya kamata gwamnati ta kara daukar mataki a kan masu Kemis da ke sayarwa mutane magani ba tare da takarda ba daga likita, wato prescription.
- A nemawa matasa sana’o’i da za su dinga dauke hankalinsu, kuma su hana su zaman kashe wando.
- A bude wuraren da za a dinga kai masu wannan lalurar ana killace su, da taimaka musu har a raba su da lalurar, wato Rehabilitation Centers a Turance.
- Ya kamata hukumar fasa kwarin kwayoyi ta kara kaimi wurin kama masu sayar da magani a bayan fage.
- Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu, su kara kaimi wurin ilimantarwa da fadakarwa, ta hanyoyi da sako zai isa zuwa ga mutane a birni da kauyuka. Idan aka bi wadannan hanyoyin ina ga za a samu saukin lamarin shaye- shaye a al’umma, koma a kawar da ita baki daya.