Shafe-shafe suna da illoli masu yawa ga ’ya mace. Na farko yakan canja wa mace launin fatarta. Fatar da ba a yi wa shafe-shafe ba ita take ba da kariya daga cututtuka da sauran kwayoyin da suke yi wa fata barazana.
Fata ta asali na ba mace garkuwa daga zafin rana. Bayan mace ta yi bilicin za ta kasance cikin yawan laulayi, ba za ta iya yawo a rana ba domin za ta ji kamar ana kwara mata ruwan zafi, saboda ta rasa fatarta ta asali da ke ba ta garkuwa daga zafin rana.
Abu na biyu shi ne, mai bilicin ba za ta samu kariya daga cutar daji (kansa) ba, wadda cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba kasafai aka fiye samun maganinta ba, cuta ce wacce take kama sassan jikin mutum, yawanci a kan yanke gabobi ko wuraren da ta kama.
Duk wannan ya samo asali ne sakamakon bilicin. Mai bilicin za ta rasa kuzari. Idan kafin ta fara bilicin tana iya yin aiki na tsawon sa’a uku ba ta gaji ba, to yanzu ba lallai ba ne ta iya na sa’o’i biyu ba, hakan ya haifar mata da nakasu, maimakon a nemo kiba sai aka iske rama.
Ba a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba, akwai illoli masu yawa da kuma tsoratarwa. Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi sani da olsa (ulcer) wanda mafi yawanci a kan dauke shi a matsayin rashin cin abinci ke kawo shi.
Daga ciki akwai kassara dukan wasu sassan jikinki masu amfani walau wadanda ake gani a zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani, kamar su: hanta da koda, wadannan duk suna tagayyara ne sakamakon illar bilicin.
Abu mafi ban takaici shi ne a karshe kwalliyar ba ta biyan kudin sabulu, domin garin neman gira an rasa idanu, a kokarin sai an zama Baturiya ko Ba’indiya, sai a koma aljana a bar tsoro a cikin mutane ko kuma in ce mujiya a cikin tsuntsaye, domin ba za a samu damar yin yawo da rana ba. haka launin fatar zai canja, fata ta yi dabbare-dabbare, ta bata goma biyar ba ta gyaru ba.
A kokarin a zama Baturiya an zama aljana, daga nan sai ta zama abin gudu da nuni ga jama’a.
A nan kuma abin duniya sai ya taru ya yi mata yawa duk ta ji duniyar ta ishe ta, lamari ya baci ke nan, dama haka duniya take idan Allah Ya yi maka rahama ka ki gode maSa, to sai ka gode wa azabarSa.
Na farko wannan shafe-shafen ba al’adar Hausawa ba ce, haka kuma ba addini ba ne, sannan mace ta sani wannan fatar tata da ta tsana har take kokarin canja ta, akwai kabilu da jinsin al’umma da yawa da idan har za ta sayar musu za su saya a kan kudi mai yawa domin sun san amfaninta amma sai ga shi a banza tana lalata tata.
Ina so a sani duk wani abu mai karanci yana da daraja a ko’ina ne, idan aka kalli fararen duniya da bakaken duniya su wa suka fi yawa? To mace baka hakan zai zama mata abin alfahari saboda tana dauke da abu mafi karanci.
Misali, da za a dauki mai farar, sannan a hada da mai bakar fata a sanya a rami a rufe, idan har ba wani ikon Allah ba mai farar fata ne zai fara rubewa, dalili kuwa shi ne bambancin yanayin halitta hade da kwayoyin halitta, domin na bakar fata sun fi juriya da kwari.
Mafita
Akwai kayan kwalliya da nau’o’in man shafawa na matan Hausawa masu gyara fata wadanda za su mayar da mace santaleliya son kowa kin wanda ya rasa irin su:
*Man kwakwa.
*Man kadanya.
*Gazal hadin zamani.
Sai mata su neme su don dawo da martabar al’adarsu da kuma nuna wa duniya cewa matan Hausawa fa ba baya ba ne domin suna da salon kwalliyarsu.
Za a iya samun Rabi’u Muhammad a wannan adireshi [email protected]