A kwanakin baya na yi wadansu rubuce-rubuce a game da wadansu fannoni na rayuwa misali na yi rubutu mai taken: Soyayyar Facebook: ’Yan mata da samari a yi hattara, da kuma Matsalar rashin iya girki ga mata da kuma Matsalar auren dole a tsakanin maza da mata da sauransu to a yau kuma zan yi tsokaci ne a kna Illar rashin haihuwa ga ma’aurata.
A gaskiya na samu sakonnin masu tarin yawa na yabo hasalima wasu sun nuna kamar na yi sara ne a kan gaba don abin da ke damun al’ummarmu a wannan zamani kenan.
To Alhamdulillah, a yau kuma zan tabo wani batu ne da ke ci wa ma’aurata tuwo a kwarya. Wannan batu kuwa shi ne na Illar rashin haihuwa ga wasu ma’aurata.
Da farko dai illar rashin haihuwa ba karamar matsala ba ce, don duk ma’auratan da suka yi aure burinsu na farko shi ne su samu karuwa. Da zarar tafiya ta fara nisa idan babu karuwa a tsakani sai ka tarar an fara shiga cikin matsala. Hakan ke sa wasu kan kauce hanya ta hanyar zuwa wajen malaman tsibbu ko bokaye da sauran hanyoyi marasa kyau duk a kokarin nemo hanyar da za su bi su samu haihuwa. Sai dai kash, ita haihuwa nufin Allah ce. Ba wayan mutum ba ne, iko ne na Allah. Idan Allah bai nufi ma’auata da haihuwa ba to duk hanyar da za su bi ba za su samu biyan bukata ba. Abu mafi muhimmanci a gare su shi ne su dangana ga Allah, su koma gare Shi wajen yin addu’a har Allah Ya biya musu bukata.
Sai dai a yankin Arewacin Najeriya musamman a kabilar Hausawa a mafi yawan lokuta an fi danganta matsalar rashin haihuwa ne a kan mata ba tare da an gudanar da wani bincike ba. A wasu lokutan za ka tarar iyalan mijin sun shiga tsangamar matar dansu saboda rashin haihuwa inda a wasu lokutan sukan bukadi dansu ya kara aure ko a a san ransa ba.
Wannan kan sa irin wannan mata shiga cikin rudani da tashin hankali da kuma neman mafita.. Hakan ke sa wasu ke fadawa cikin bin wadansu hanyoyi marasa kyau duk da niyyar neman samun haihuwa. Kai wasu matan kan ziyarci bokaye ko malam tsibbu da niyyar su samar masu mafita. Irin wadannan bokaye kan yi amfani da irin wannan dama wajen yaudarar irin wadannan mata wasu lokuta har su rika yin lalata da su wai ta haka ne za su samar musu maganin da zai sa su rika haihuwa.
Na taba samun wani labari makamancin haka na wata mata da ta dade ba ta haihuwa kuma dangin mijinta suka tsane ta. Hankalinta ya tashi ne bayan sun shafe shekara 10 da aure ba tare da sun haihu ba. Wannan mata sai ta kasa mayar da al’amarinta ga Allah, sai ta rika yin shigar burtu tana ziyartar bokaye da malaman tsibbu da niyyar ta samu haihuwa.
Nan fa irin wadannan bokaye suka yaudari wannan mata suka rika kwanciya da ita ba adadi wai da niyyar su yi mata ciki don ta yi wa mijin kazafi cewa na mijinta ne. Abu ya ki ci, ya kuma ki cinyewa daga baya asirinta ya tonu mijin ya sake ta. Takaici ya ishe ta, tilas ta sa ta canza gari ta koma wani wuri don ta samu sauki saboda irin tsangwa da kuma tsanar da ake nuna mata daga wajen danginta da kuma sauran al’ummar da suka santa.
Ashe matsalar rashin haihuwar daga wajen tsohon mijinta ne, tun da ba su yi tunanin zuwa asibiti don a duba lafiyarsu su biyun ba. Bayan mijinta ya rabu da ita ne sai ya sake yin aure, nan ma ya shafe kimanin shekara 10 ba tare da ya samu haihuwa ba. Ita ma matar ta biyu da ta gaji da rashin haihuwa sai ta nemi mijin ya sake ta, don ita ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba tare da sun samu karuwa ba, don ita burinta a rayuwa shi ne ta haihu musamman ma ta samu karuwar ’ya mace.
Bayan mijin ya rabu da ita ne sai ta sake yin wani aure, cikin ikon Allah kafin shekara guda sai ta haifi ’yan biyu. Ita ma waccan matar da ya saka tun da farko Allah Ya sa ta shiryu kuma ta yi wani sabon aure a wani gari, ita ma kafin ka ce wani abu ta samu karuwar ’yan biyu.
To cikin ikon Allah mijin nasu nan ido ya raina fata, ya gano ashe matsalar daga wajensa take. Nan ya shiga neman magani da kuma rokon Allah. Allah Maji rokon bawa, cikin RahamarSa shi ma bayan ya sake wani auren ba a dade ba sai ya samu karuwar ’yan biyu.
Ka ga wannan wata aya ce Allah Ya nuna a nan. Abin da ake nufi a nan shi ne idan irin hakan ta faru to ma’aurata su rika mayar da al’amarinsu ga Allah ta hanyar yin addu’o’i.
Sannan a wasu lokuta watakila rashin haihuwar ga wasu ma’auratan taamkar rahama ce daga Allah, don sau da yawa wasu kan haifi ’ya’yan ne ba tare da ba su kyakkyawar tarbiyya ba, da hakan ke sa su gurbata al’umma. To a nan ina amfanin irin wannan haihuwa?
Fatarmu da addu’armu dai ita ce Allah Ya ba ma’aurata zuri’a tagari wacce za ta taimaka musu da sauran al’umma har su yi alfahari da su. Ga wadanda kuma ba su samu ba, muna yi musu addu’ar Allah Ya ba su, idan kuma ba su samu ba to su danganta su mika al’amarinsu ga Allah, don Shi ne mabuwayi da daukaka.
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883