Da soyayyarsu ta yi karfi ne, sai suka yanke shawarar yin aure. Abin ka da wanda ya yi nisa, bai nemi shawarar mahaifiyarsa ba sai ya amince ya auri wannan yarinya. Bai sanar da mahaifiyarsa ba sai ana gab da daura masa aure da ita. Duk da haka mahaifiyarsa ta amince ya auri wannan yarinya, duk da a ranta ba haka ta so ba, don ba ta san tarbiyyarta ko asalinta ba. Ta yi haka ne don gudun batawa danta rai.
Bayan an sha biki, sai ita ma wannan sabuwar amarya ta tare a gidan da danta ke zaune tare da mahaifiyarsa. Abin takaici da mamaki shi ne ba a dauki lokaci mai tsawo ba, sai amaryar ta fara tsangwamar mahaifiyar mijin, ta hanyar nuna mata kyama, a wasu lokutan ma har tsawa take dakawa mahaifiyar a gaban dan, ba tare da ya ce uffan ko nuna wata damuwa ba.
Haka dai suka ci gaba da zama, mahaifiyar tana hakuri alhali danta ya kasa yin wani katabus game da irin cin fuskar da matarsa ke yi mata, a gabansa ko a bayan idonsa.
Ba a dade ba sai matar ta nemi danta ya dauko mata mai aikin gida, don ita ba za ta iya ci gaba da jure yin aikin gida ba, hasalima ita hutu ta zo yi gidansa, wai ba bauta ba.
Bayan an dauko ’yar aikin ce sai wata rana matar ta ba mahaifiyar izinin ta kwashe kayanta daga bangaren gidan ta koma bangaren yara (boys kuarters) don a cewarta, ’yar aikin ce za ta zauna a dakin da take.
Abin mamaki, mijinta watau dan matar a gabansa matar tasa ta ba mahaifiyarsa wannan umarci, amma ya kasa cewa uffan. Hakan kuwa aka yi, mahaifiyar na kuka ta kwashe ’yan komatsenta ta koma bangaren yara a gidan. Da yake mai hakuri ce, ba ta ce komai ba haka ta koma can ba tare da neman wata husuma ba.
Haka suka ci gaba da zama a haka a cikin gidan. Wata rana mahaifiyar ta fita unguwa, ba ta koma ba sai da kusan Magbriba. Tana shiga gidan sai ta ga an fito mata da kaya daga dakinta an zube su a tsakar gida. Har za ta wuce dakinta sai ta yanke shawarar ta yi wa danta da matarsa sallama, don ta nuna musu ta dawo daga unguwa. Ai matar danta na jin haka sai ta fito yayin da mijinta ke biye tana yi wa mahaifiyar masifa ta nuna cewa sun yanke shawarar korarta daga gidan ne, wai ta takurawa rayuwarsu, hasalima tana sanya musu ido don haka ba sa samun sakewa.
Abu kamar almara, ta kalli danta amma ta ga ya yi tsit, ya kasa cewa uffan, yadda a gabansa matarsa ke ci mata mutunci alhali ya kasa cewa komai. Da ta tambayi matar wurin da za ta koma, sai ta ce ita wannan ba matsalarta ba ce, duk inda za ta koma, ta koma, amma ba za ta taba amincewa ta sake kwana a gidan ba.
Mahaifiyar na kuka, ta kwashe ’yan komatsanta ta nufi gidan wata kawarta da ke makwabtaka da su. Abin ya daure wa makwabciyarsu kai da ta ji abin da danta da matarsa suka yi wa mahaifiyarsu. Nan take makwabciyar ta amince matar ta koma wajenta su ci gaba da zama har ta samu mafita. Washegari ne ta buga wa ’yarta waya wacce take aure a wata unguwa ta sanar da ita halin da take ciki sannan ta nemi izini tana son ta koma wajenta da zama tun da danta da matarsa sun ci mata mutunci. Ita ma sai ta nuna hakan ba zai taba yiwuwa ba, don ta nuna hasalima a lokacin da ta taba kai musu wata ziyara wai ta takurawa mijinta ne, ballantana yanzu da take neman ta koma wajensu ta zauna a matsayin dindindin.
Nan take ta sake fashewa da kuka da ta ji yadda ’yar cikinta ita ma ta fada mata irin wadannan miyagun kalamai. Nan dai makwabciyar ta lallasheta da cewa su ci gaba da zama har illa masha Allahu.
Mutanen unguwa da suka ji wannan labari ne suka yi karo-karo wajen gyarawa wannan mata dakin da aka ba ta a gidan makwabciyar. Kai ka ce tamkar dakin wata sabuwar amarya ce. Haka suka rika tururuwar kai mata abinci da kuma zuwa wajenta suna taya ta hira don dauke mata kewa ta hanyar kwantar mata da hankali.
A gaskiya ta samu kwanciyar hankali, amma duk abin nan da ake yi danta ko ’yarta babu wanda ya damu ya san wurin da take ballantana su kai mata ziyara.
Ana cikin haka ne sai rashin lafiya mai tsanani ya kama matar, inda mutanen unguwa suka yi karo-karo aka kai ta asibiti. Ciwon ya yi matukar tsananin, inda al’ummar unguwar suka rika yin tururuwa wajen gaisheta amma danta ko ’yarta babu wanda ya ziyarce ta.
Allahu Akbar! duk da irin wannan hali da mahaifiyar ta shiga ba abin da take yi wa ’ya’yanta sai addu’ar Allah ya shiryar da su, Ya sa su dawo kan hanya madaidaciya duk da irin cin fuskar da suka yi mata.
Sai dai labarin ya nuna mahaifiyar Allah Ya karbi ranta kuma aka yi jana’izarta ba tare da danta ko kanwarsa sun halarta ba. Daga baya ne ma aka sanar da su halin da mahaifiyarsu ta shiga da kuma yadda ta rasun.
Sai dai ko ba a fada ba, ka san wadannan ’ya’ya sai sun hadu da fushin Allah, tun a nan duniya, kafin a je gobe kiyama.
Wulakancin da suka yi wa mahaifiyarsu kafin ta rasu, zai zama abin wasan yara akan yadda za su gamu da masifu iri-iri kafin su bar duniya.
Na tabbata ko da wadannan ’ya’ya nata sun tuba, sai sun ga jarrabawa iri-iri kafin su mutu saboda irin wulakancin da suka yi wa mahaifiyarsu da hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Don haka wannan wani kalubale ne da kuma nasiha ga matasanmu maza da mata musamman masu fifita matansu akan iyaye ko kuma masu bijire wa iyayensu.
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883